Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayar da umarnin bayar da umarnin neman lafiya kyauta a duk asibitocin gwamnati da ke fadin jihar.
Kwamishinan Lafiya da Ayyuka na jihar, Farfesa Mohammed Arab ne, ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da magungunan a Maiduguri.
Wannan mataki na zuwa ne a yayin da jama’a suka shiga wani yanayi sanadiyyar karancin takardun kudi, inda gwamnan ya bayar da magungunan da kudinsu ya kai Naira miliyan 300 da sauran kayayyakin jinya zuwa asibitocin gwamnati don a raba wa mabukata.
Arab, ya ce kayyakin sun hada da magungunan cututtuka masu yaduwa, kayan haihuwa da sauran kayayyakin kiwon lafiya.
Kwamishinan ya umurci daraktocin kiwon lafiya da manyan jami’an kiwon lafiya da ke Maiduguri da su shirya karbar kasonsu.
Arab ya ce dole ne a raba magungunan kyauta ga marasa lafiya da ba su da kudi a hannu ko kuma wadanda ke da matsala wajen samun kudin biyan magungunansu.
“Dole jami’ai su raba magungunan kyauta ga wadanda ba su da kudi ko matsalar samun kudi kamar yadda Zulum ya umarta.”
Balarabe a madadin ma’aikatan lafiyan jihar, ya gode wa Zulum bisa karamcin da ya yi wa mutanen jihar a wannan mawuyancin hali da ake ciki.
Da yake jawabi a madadin sauran daraktocin kiwon lafiya, Daraktan Kula da Lafiya na Asibitin Kwararru na jihar, Dokta Baba Shehu Mohammed, ya yaba da wannan mataki na gwamnatin jihar.
“Ba ma jin dadin ganin marasa lafiya sun kasa biyan kudin ganin likita ko siyan magunguna,” in ji shi.