✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zulum: Babu harin da aka kai wa Gwamnan Borno

Hadimin gwamna Zulum ya musanta rade-radin da ake na an kai wa gwamnan hari a karshen makon da ya gabata.

Hadimin Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya karyata rahotannin da ke yawo cewa an kai wa tagawar gwamnan hari.

Da yake karyata labarin, kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau, ya ce Gwamna Zulum ya je Baga duba wasu ayyuka kuma ya dawo garin Maiduguri lafiya.

“Za mu karyata labaran da wasu kafofi ke yadawa cewar an kai wa Gwamna Zulum hari.

“Ba a kai wa Gwamna Zulum ko wata tawagarsa hari ba”, inji jami’in.

Gwamnan ya ziyarci garin Baga ranar Asabar zuwa Lahadi don duba yadda rabon kayan abinci da kudi ke gudana ga mutum 5,000 da aka ware.

Ya kara da cewa babu labari mai kama da haka kuma gwamnatin jihar ba ta sanar da wata kafa faruwar wani abu mai kama da hakan ba.

A nasa bangaren, Gwamna Zulum, ya jinjina wa rundunar soji da kuma sauran jama’a da ke taimakawa wajen yaki da ayyukan ’yan tada kayar baya a jihar ta Borno.