Hadimin Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya karyata rahotannin da ke yawo cewa an kai wa tagawar gwamnan hari.
Da yake karyata labarin, kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau, ya ce Gwamna Zulum ya je Baga duba wasu ayyuka kuma ya dawo garin Maiduguri lafiya.
- Za a iya magance rikicin Boko Haram a siyasance – Zulum
- Zulum ya raba wa mabukata 8,000 tallafi
- Motocin yaki kirar Najeriya sun inganta yaki da Boko Haram
- Giwaye na barazana ga noman abinci a Borno
“Za mu karyata labaran da wasu kafofi ke yadawa cewar an kai wa Gwamna Zulum hari.
“Ba a kai wa Gwamna Zulum ko wata tawagarsa hari ba”, inji jami’in.
Gwamnan ya ziyarci garin Baga ranar Asabar zuwa Lahadi don duba yadda rabon kayan abinci da kudi ke gudana ga mutum 5,000 da aka ware.
Ya kara da cewa babu labari mai kama da haka kuma gwamnatin jihar ba ta sanar da wata kafa faruwar wani abu mai kama da hakan ba.
A nasa bangaren, Gwamna Zulum, ya jinjina wa rundunar soji da kuma sauran jama’a da ke taimakawa wajen yaki da ayyukan ’yan tada kayar baya a jihar ta Borno.