✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zuciyarku za ta yi kunci –Klopp ga Mane da Salah

Ba wanda ya taba daukar Kofin Afirka tsakanin Mane da Salah

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, ya shaida wa fitattun ’yan wasan kungiyar, Sadio Mane da Mohamed Salah, cewa suna daf da cimma wani “gagarumin lamari”.

Klopp ya bayyana musu hakan ne yayin da ake shirye-shiryen karawa a wasan karshe na Gasar Cin Kofin Afirka (AFCON) a tsakanin Senegal da Masar.

Sai dai kuma kocin, kamar yadda jaridar Mirror ta rawaito, ya gargadi ’yan wasan cewa zuciyar dayansu za ta yi kunci a karshen fafatawar, wadda kasashensu za su yi a filin wasan na Ahmadou Ahidjo da ke Yaoundé, babban birnin Kamaru.

“Ba abu ba ne mai sauki, domin a karshe daya daga cikinsu zai yi farin ciki, dayan kuma akasin haka.

“Amma dai wata dama ce ta cimma wani gagarumin lamari”, inji Klopp.

Tawagar Masar, a karkashin jagorancin Salah, za ta yi fito-na-fito ne da tawagar Senegal, wadda Mane ke jagoranta, don daukar kofin da shi ne mafi darajar sakamakon kwazo a fagen wasannin motsa jiki a Afirka.

Cikar buri

Duk da shaharar da kowannensu ya yi a fagen kwallon kafa dai, ba wanda ya taba daga kofin na Afirka a cikinsu.

Saura kiris Mane ya daga kofin a gasar da aka yi shekaru biyu da rabi da suka wuce, amma ya ga samu ya kuma ga rashi – a wancan lokacin Riyad Mahrez na Manchester City ne ya daga kofin tare da tawagar Aljeriya.

Shi ma Salah ya dandana dacin rashi a wasan karshe lokacin da ana saura minti kadan a tashi Vincent Aboubakar ya wulla kwallon da ya bai wa Kamaru nasara a kan Masar kusan shekaru biyar da suka wuce a Gabon.

Ana kallon wannan wasa na ranar Lahadi a matsayin karon batta tsakanin Sadio Mane da Mohamed Salah, wadanda, bayan kasancewarsu tare a kungiyar Liverpool, abokan juna ne.

Duka ’yan wasan biyu sun bayyana matukar burinsu na daga kofin.

Ranar Asabar Kamaru ta yi nasarar kwato matsayi na uku a gasar daga hannun Burkina Faso ana saura minti kadan a tashi – bayan ta farke kwallo biyun da Burkina Faso ke gabanta da su, ta lashe bugun fanareti.