✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zubairu Balannaji ya lashe gasar gajerun labarai ta Kano ta 2024

Gwarzon ya ce lashe gasar ya ba shi ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da bunƙasa adabin Hausa.

Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta sanar da Zubairu Musa Balannaji a matsayin wanda ya lashe gasar gajerun labarai ta shekarar 2024.

Hukumar ta ayyana labarinsa Bahaushiyar Al’ada a matsayin wanda ya zama na ɗaya cikin labarai 50 da suka shiga gasar.

Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai na Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a ranar Talata.

Ya bayyana cewa gasar ta kasance wata dama mai matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa fasahar rubutu da raya adabin Hausa.

An bayyana sakamakon ne a ɗakin taro na Malam Aminu Kano da ke Mumbayya, inda Shugabar Kwamitin Gasar, Farfesa Halima Abdulkadir Dangambo, ta bayyana Balannaji a matsayin wanda ya lashe gasar.

Labarinsa ya yi zarra a kan sauran labaran saboda ƙwarewarsa a isar da saƙon adabi da tsantsar Bahaushiyar al’ada.

Danladi Haruna (Zakariyya), ya zo na biyu da labarinsa mai taken Gadon Gida Sai da Horo, yayin da Hauwa Shehu ta zo a matsayi na uku da labarinta mai taken Bahaushe Mai Arziƙi Ne.

Shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha, ya nuna farin cikinsa kan yadda gasar ta gudana cikin nasara.

Ya kuma taya waɗanda suka samu nasara murna, inda ya bayyana gasar a matsayin wata dama ta bunƙasa fasahar rubutu a tsakanin matasa da marubuta.

A nasa ɓangaren, Zubairu Musa Balannaji ya gode wa Allah tare da nuna jin daɗinsa kan wannan gagarumar nasara da ya samu.

Ya ce wannan gasar ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da rubuce-rubuce da nufin bunƙasa adabin Hausa.

Hukumar ta bai wa waɗanda suka yi nasara kyaututtuka, inda wanda ya zo na ɗaya ya samu Naira 500,000, wanda ya zo na biyu ya samu Naira 300,000, sai wadda ta zo ta uku ta a samu Naira 200,000.

Wannan na daga cikin ƙoƙarin hukumar na ƙara wa waɗanda suka lashe gasar ƙwarin gwiwa a ƙoƙarinsu na bunƙasa adabin Hausa.