Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar yadda aka tsara a ranar Asabar.
Abba ya jaddada cewa Gwamnatinsa da Hukumar Zaɓe ta Jihar Kano (KANSIEC) a shirye suke a gudanar da zaɓen da kuma rantsar da waɗanda suka yi nasara.
Ya ce suna da hujja da doka ta ba su ikon gudanar da zaɓen a ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar.
Abba ya bayyana haka ne a taron mika tuta ga ’yan takarar shugabancin ƙaramar hukuma na Jam’iyyar NNPP da ya gudana a Filin Wasa na Dani Abacha da ke Kofar Mata.
Maganar tasa ta zo ne bayan umarnin Babbar Kotun Tarayya da ta dakatar da KANSIEC daga gudanar da zaɓen.
Mai Shari’a Simon Ademola ya kuma sauke Shugaban hukumar tare da ba rushe majalisar daraktocin hukumar, bisa hujjar cewa mambobin Jam’iyyar NNPP ne kuma hakan ya saɓa doka.
A ranar Juma’ar nan kuma ne Babbar Kotun Jihar Kano za ta yanke hukunci kan ƙarar da KANSIEC shigar kan jam’iyyun adawa 19 da ke a neman hana zaɓen.
Ana iya tuna cewa a ranar 26 ga watan Satumba kotun ta hana jam’iyyun yin duk wani abu da zai kawo cikas ga gudanar da zaben.