Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta dakatar da tattara sakamakon zaɓen Gwamnan Jihar Edo, wanda aka gudanar a ranar Asabar.
Babban jami’in tattara sakamako na INEC, Farfesa Faruk Adamu Kuta, ya bayyana cewa an dakatar da tattara sakamakon ne saboda ba a samu sakamako daga ƙananan hukumomin Oredo da Ikpoba Okha ba.
- Zaɓen Edo: Magoya bayan PDP sun fara zanga-zanga
- Tsadar Rayuwa: Matar Tinubu ta raba wa ɗalibai littafan rubutu a Nasawara
“Jami’an tattara sakamako daga waɗannan ƙananan hukumomi biyu har yanzu suna kan aiki, don haka ba za mu ci gaba da tattara sakamako ba sai mun samu rahoto daga wajensu,” in ji shi.
Ana sa ran ci gaba da tattara sakamakon kafin daren ranar Lahadi, domin bayyana ɗan takarar da ya lashe zaɓen.
A halin yanzu, sakamakon daga ƙananan hukumomi 16 daga cikin 18 ya nuna cewa jam’iyyar APC ke kan gaba, sai jam’iyyar PDP.
Ga sakamakon da kowace jami’yya ta samu:
– APC: ƙuri’u 244,549
– PDP: ƙuri’u 187,880
– LP: ƙuri’u 21,420
Aminiya, ta ruwaito cewar jam’iyyar APC ce kan gaba da ƙuri’u 56,669 yayin da ake jiran sauran sakamako daga ƙananan hukumomi biyu da suka fi yawan jama’a a Jihar Edo.