An yi muhawara mai zafin gaske a tsakanin Sanatoci kan kudirin neman kafa Hukumar Kula da Ayyukan Dakarun Soji yayin zaman Majalisar Dattawa da ya gudana a ranar Laraba.
Sanata Enyinnaya Abaribe wanda yake sahun gaba na muhawarar, ya ce Hukumar da ake neman kafawa za ta tabbatar da cewa an yi la’akari da duk wani tanade-tanaden dokokin da’ar ma’aikata da ke cikin kundin tsarin mulkin kasa yayin nadin manyan hafsohin tsaro.
- An dage auren amaryar da ta bata gab da bikinta
- ’Yan bindiga sun bude wuta a kan ayarin Sarkin Birnin Gwari
’Yan majalisar da suka goyi bayan wannan kudiri sun bayar da hujjar cewa kudirin yana kan turba ta kundin tsarin mulkin kasa kuma ya kamata majalisar ta yi duk wata mai yiwuwa a kansa kamar yadda dokar kasa ta ba ta dama.
Wasu ’yan majalisar da suka ki yi wa kudirin tawaye sun riki cewa kafa Hukumar zai jefa siyasa a cikin lamarin ayyukan soji a kasar wanda kuma hakan babban hatsari ne ga zaman lafiya da hadin kai a kasar.
Bayan wannan zazzafar muhawara ce Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Ahmed Lawan, ya nemi da a yi kuri’ar baka, inda masu adawa da kudirin suka rinjayi masu goyon bayansa.
Cikin hanzari Sanata Abaribe ya yi zumbur ya tashi yana cewa, akwai doka mai lamba 73 da ta bai wa kowane Sanata damar kalubalantar hukuncin da shugaban majalisar ya zartar, don haka ya nemi da a kada kuri’a a kan kudirin.
Sai kuwa Shugaban Makalisar ya kada baki yana cewa hukuncin ba ra’ayin kansa bane, “ba ra’ayi na ba ne, masu adawa da kudirin suka rinjayi masu goyon bayansa.”
Wakilinmu ya ruwaito cewa, Sanata Abaribe ya cije a kan cewa yana da cikakken ’yancin neman a kada kuri’a a kan kudirin.
A karshe dai Sanata James Manager na jam’iyyar PDP mai wakiltar shiyyar Delta ta Kudu, ya shawarci Shugaban Majalisar da ya bari a kada kuri’a, inda bayan wasu ’yan mintuna zaman majalisar ya koma ta bayan labule.