✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zazzabin Lassa ya kashe mutum 59, ya harbi 358 a sati 6

NCDC ta ce adadin masu kamuwa da zazzabin Lassa na karuwa

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta tabbatar da mutuwar mutum 59 sakamakon kamuwa da zazzabin Lassa a sati shida da suka gabata.

Rahoto da NCDC ta fitar a ranar Laraba ya kara da cewa mutum 358 sun kamu da cutar a wasu kananan hukumomi 65 na jihohi 19 da ke kasar nan.

Rahoton ya bayyana cewa ma’aikatan lafiya bakwai a jihohin Bauchi, Ondo da Edo sun kamu da cutar a cikin mako shidan da suka gabata.

Har wa yau hukumar ta ce adadin masu kamuwa da cutar daga sati shidan da suka gabata na karuwa, inda aka samu karin mutum 77.

Mutanen da suka kamu da cutar ta zazzabin Lassa sun fito ne daga jihohin Ondo, Edo, Bauchi, Ebonyi, Taraba, Enugu, Binuwe, Nasarawa, Kogi, Neja da kuma Abuja.

Rahoton ya bayyana cewa daga satin farko zuwa na shida na sabuwar shekarar adadin mutanen da suka mutu da cutar ya karu da kashi 22.9 cikin 100.

NCDC ta ce tuni aka fitar sanarwar ga cibiyoyin lafiya kan yadda za a magance cutar da kuma dauki da za a bayar ga mutanen da suka harbu da ita.