✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zazzabin Lassa ya hallaka mutum daya, 81sun kamu da shi a Adamawa

Mutum daya ya rasa ransa sakamakon kamuwa da cutar zazzabin bera (Lassa) sannan 81 na jinya a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke…

Mutum daya ya rasa ransa sakamakon kamuwa da cutar zazzabin bera (Lassa) sannan 81 na jinya a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Yola fadar Jihar Adamawa.

Aminiya ta gana da Kwamishinar Lafiya ta Jihar, Hajiya Fati Abubakar Atiku game da bullar cutar inda ta ce cutar ta shigo Yola ne inda wani ma’aikacintsaro mai kimanin shekara 46 da yake aiki a Gembu a Jihar Taraba ya fara kamuwa da cutar kuma ya shigo Jihar Adamawa domin neman magani a asibitin FMC a ranar 30 ga Maris din da ya gabata.

“Bayan kwana biyu, zazzabin nasa ya yi tsanani sai ya sake komawa asibitin aka rike shi,” inji ta.

Bincike ya nuna cewa likitoci sun gudanar da gwaje-gwaje inda suka gano cewa yana dauke da cutar zazzabin Lassa amma kafin a fara yi masa magani sai rai ya yi halinsa a ranar 13 ga Afrilun nan.

Hajiya Fati Atiku ta gargadi jama’a kan su rika hanzarta zuwa asibiti da zarar sun ji alamun zazzabi, kuma ta ce ana kamuwa da cutar ta hanyoyi hada jini da amai da fitsari ko bahayar majinyacin ya shafi wani.

Ta ce za ta yi iya kokarinta wajen ganin an magance cutar a jihar.

Ma’aikatan lafiya sun bukaci jama’a su rage baza abinci a rana kuma su rika kula da tsabtace gidajensu da rufe abinci kuma idan gida akwai beraye a yi kokarin kashe su cikin gaggawa.