✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zazzabin Lassa ya bulla a Gombe

Rahotanni sun gano an samu mace daya mai dauke da cutar a jihar.

Wasu rahotanni daga Jihar Gombe sun bayyana cewar an samu bullar cutar zazzabin Lassa a jihar.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Habu Dahiru wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba ya ce an gano wata mata dauke da cutar.

“Lokacin da ta ke dawowa Gombe sai ta fara zazzabi sannan aka kwantar da ita a Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya da ke Gombe.

“Bayan fitowar sakamakon gwajin da ta aka yi mata an tabbatar tana dauke da zazzabin Lassa.

“An kafa tawagar bayar da agajin gaggawa na jiha tare da samar da magunguna don hana yaduwar cutar,” in ji shi.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta samar da dakin gwaje-gwaje da kuma wajen killace masu dauke da cutar.

“Mun kuma kafa cibiyar kebe masu cutar a shiyoyi uku na jihar a matsayin wani mataki ka dakile cutar,” in ji shi.

Kwamishinan ya kara da cewa, Kwamitin da aka kafa zai ci gaba da zagaye domin gano wadanda suka kamu da cutar tare da wayar da kan jama’a kan alamun zazzabin Lassa.

“Samun mutum daya dauke da zazzabin Lassa, na nufin annoba ta barke,” in ji Dahiru.

Ya yi kira da a rika tsaftace muhalli don dakile yaduwar cutar zazzabin Lassa a Jihar Gombe.

“Tsaftar jiki da ta muhalli da kuma tabbatar da kiyaye matakan kariya daga cutar Lassa,” in ji Dahiru.