Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC), ta sanar da samun karin mutanen da suka mutu a sanadiyar kamuwa da cutar Zazzabin Lassa a jihohi biyu.
Kawo yanzu dai adadin mutanen da suka mutu a sakamakon cutar tun daga farkon 2021 ya kai 92.
- COVID-19 ta sake kama mutum 1,547 a Najeriya — NCDC
- An rufe wani Masallaci saboda tunzura jama’a a Faransa
Rahoton da NCDC ta fitar ya nuna mutum 454 ne suka harbu da cutar a kananan hukumomi 66 da ke jihohi 16 a Najeriya, ciki har da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Jihohin sun hada da Edo, inda mutum 197 suka harbu, sai Ondo na da 159, Taraba kuma 21.
Sauran jihohin sun hada da Bauchi da Ebonyi masu mutum 18 kowannensu, kamar yadda NCDC ta bayyana a shafinta na intanet.
A mace-macen da aka samu a baya-bayan nan kuwa, rahoton na NCDC ya nuna cewa an samu karin mutum uku da suka mutu a sakamakon cutar.
NCDC ta sake bayyana cewa jihar Bauchi na daga cikin jihohin da ke fuskantar barazana daga zazzabin na Lassa a yankin Arewacin Najeriya.