✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 26 sun kamu da Zazzabin Lassa a Edo

Kwamishinar ta gargadi mutane da su kasance masu kula da lafiyar jikinsu.

Gwamnatin Jihar Edo ta ce mutum 26 ne aka tabbatar sun kamu da cutar zazzabin Lassa.

Kwamishinan Lafiya ta jihar, Farfesa Obehi Akoria ce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Laraba a Benin.

Akoria ta ce yawaitar karuwar masu cutar a jihar abun damuwa ne.

Don haka ta bukaci jama’ar jihar da su kiyaye matakan kariya domin kare kansu da kuma ‘yan uwansu daga kamuwa da cutar.

Sai dai ta ce zazzabin Lassa cuta ce da za a iya maganinta ta hanyar rigakafi.

“Jihar Edo ba ta daga cikin jihohin da suka fi yawaitar wannan cuta.

“Wannan ya nuna cewa ayyukan da muke yi na hana mutane kamuwa cutar zazzabin Lassa.

“Zazzabin Lassa cuta ce da kwayar cutar Lassa ke haifarwa kuma ana kamuwa da ita ta hanyar cudanya da mutane ko fitsari ko kuma taba beran da ke dauke da cutar.

“Haka kuma ana iya yada ta ta hanyar karin jini, fitsari, maniyyi ko nonon mutanen da suka kamu da cutar,” in ji ta.

Akoria, ta lissafa alamomin cutar kamar zazzabi, ciwon kai, rashin kuzari, ciwon kirji, ciwon makogwaro, amai da gudawa da zubar jini idan ciwon ya yi tsanani.

Ta gargadi mazauna jihar da su guji kona daji, zubar da shara barkatai da kuma kula da tsaftar jiki.

Ta kuma yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya da su daina kula da cututtukan da ba su da masaniya a kai.

“Ya kamata su gaggauta gabatar da irin wadannan cututtukan saboda kamo bakin zarensu da wuri da kuma hana yaduwarsu.”