Gwamnatin jihar Bauchi ta ce akalla mutane takwas ne aka tabbatar da rasuwarsu bayan barkewar zazzabi mai zafi a karamar hukumar Ganjuwa dake jihar.
Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar, Dakta Rilwanu Muhammad ya shaidawa ‘yan jarida ranar Litinin a Bauchi cewa an sami mace-macen ne a makon da ya gabata.
“Yayin zagayen rigakafin da muka yi a makon da ya gabata, mun sami rahoton mutuwar mutum takwas sakamakon zazzabi mai zafi, amma bayan an dauki gwajin jikinsu sai sakamakon ya nuna cewa suna dauke da zazzabin,” inji shi.
Dakta Rilwanu ya kuma yi bayanin cewa an sami mace-macen ne a kauyuka biyu na karamar hukumar.
Ya ce tuni hukumar ta kaddamar da wani kwamitin kar-ta-kwana wanda ya kunshi masu zirga-zirga domin gwaji da gano masu dauke da cutar.
Daga nan sai ya bayyana cewa tuni gwamnatin tarayya ta tsara gudanar da allurar rigakafi a kananan hukumomi 19 na jihar daga watan Fabrairun 2021.
Shugaban ya kuma yi kira ga jama’a kan su ci gaba da kiyaye tsaftar jikinsu da ta muhallansu domin kare kansu daga kamuwa da cututtukan.
Idan za a iya tunawa, ko a bara sai da akalla mutane 77 suka mutu sakamakon zazzabin a jihar.