Zauren Malaman Addinin Musulunci na Nijeriya ya ce yana goyon bayan aurar da ‘yan mata marayu 100 da aka shirya yi a Jihar Neja.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da zauren ya fitar ranar Juma’a, yana mai cewa aurar da ’yan matan marayu zai taimaka musu ne wajen tsare mutuncinsu kuma ba zai hana su karatu ba.
- Gwamnati da NLC za su sake zama kan mafi ƙarancin albashin ma’aikata
- Jemagu: Garin da maza ba su auren macen da ta wuce sakandare a Kano
Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da Ministar Mata ta Nijeriya, Barista Uju Kennedy Ohanenye take cewa ma’aikatarta ta shirya bai wa ’yan matan 100 ‘sabuwar rayuwa’ da mayar da su makaranta da kuma koya musu sana’o’i.
Zauren malaman ya ce duba da matsalar tsaro da matsin tattalin arziki da wasu yankunan Arewacin Najeriya ke fuskanta, ɗaukar nauyin aure wani nau’i ne na tallafa wa marasa ƙarfi
“A shekarun baya-bayan nan Jihar Neja da wasu jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya na fama da matsalar tsaro da ’yan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa.
“Wannan lamarin ya shafi rayuwar mutanen yankin, iyalai da dama sun rasa iyayensu, kan haka ne shugabannin al’ummar yankin ke ƙoƙarin magance musu wahalhalun da suke fuskanta ta ɓangarori daban-daban, kamar yadda kakakin majalisar dokokin Neja ya yi yunƙurin yi,” in ji sanarwar.
“A matsayinmu na musulmi muna ƙoƙarin yin abubuwa kamar yadda shari’a ta tanadar, su kansu ’yan matan sun zaɓi su yi aure, a maimakon su faɗa karuwanci ko a yi safararsu zuwa Turai kamar yadda wasu da ba su da hali ke yi don rage wa kansu matsin rayuwa,” kamar yadda sanarwar ta yi bayani.
“Abin da minista ta yi nuna wariya ne da wargaza abu mai kyau da rashin ƙwarewar aiki da kuma ƙabilanci, domin kundin tsarin mulkin Najeriya ya amince da ’yancin addinin tare da amincewa ta shari’ar musulunci da ta amince da aure,” in ji sanarwar.
Tun da farko Ministar ta yi zargin cewa matan da za a aurar ba su isa shekarun aure ba, inda ta shigar da kara kotu tana neman ta hana Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, Abdulmalik Sarkindaji, wanda ya ɗauki nauyin lamarin, aurar da su.
Sai dai sanarwar malaman, wacce shugaban zauren, Malam Aminu Inuwa da sakatarensa, Injiniya Basheer Adamu Aliyu suka sanya wa hannu, ta ce kamata ya yi ministar mata ta Nijeriya ta fahimci mabambantan al’adu na kasar kafin ɗaukar irin wannan mataki.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa abin da Kakakin Majalisar ke shirin yi abin a yaba be ba na kushewa ba kuma ya yi dukkan abin da ya kamata, don haka ya kamata a jinjina masa.
Ta ce a matsayinsu na Musulmai, mafi yawancin mutane sun yi riƙo da koyarwar addininsu da tanade-tanaden shari’a.
“Hatta mutanen da ta’addanci ya shafa sun gwammace su kiyaye tsarin aure maimakon shiga harkokin karuwanci da safarar mutane zuwa Turai, kamar yadda wasu ‘yan Nijeriya da ba za su iya jure matsin tattalin arziki ba suke yi.
“Kundin Tsarin Mulkin Niijeriya ya ba da ‘yancin addini ya kuma san da tanade-tanade Shari’a da ya amince da auren mace da namiji,” a cewar sanarwar.
A cewar sanarwar, kamata ya yi ministar ta yi amfani da ofishinta wajen magance laifuka da ake aikatawa kan mata a faɗin Nijeriya, maimakon hana shirin aurar da ‘yan mata marayu.
“Waɗannan laifukan sun haɗa da yadda wasu mata da ‘yan ƙungiyoyin asiri suke safarar ‘yan mata zuwa Turai, da gidajen ƙyanƙyasar jarirai da ake yi wa mata ciki suna haifar yara ana sayarwa a Kudu Maso Gabas, da kuma yadda ake sace yara daga Arewa zuwa Kudu Maso Gabas don a yi miyagun ayyuka da su,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne limamai a masallatan Juma’a na Jihar Neja da wajen jihar suka sanar da cikakken goyon bayan tallafin da Kakakin Majalisar Dokokin ya bayar wajen aurar da ’yan matan marayu, bayan da aka nemi taimakonsa saboda yadda maraici ya hana aurar da su.
A cikin makon da ke ƙarewa ne Ministar Mata ta shigar da wata ƙara kotu inda ta nemi a dakatar da aurar da ’yan matan 100 da aka shirya yi a jihar ta Neja har sai an yi bincike kan shekarunsu da kuma tabbatar da cewa ba auren dole za a yi musu ba, kamar yadda sanarwar ma’aikatar ta bayyana.
Ministar ta ce idan taimakon ’yan matan kakakin majalisar ke son yi, me zai hana ya ɗauki nauyin karatunsu, ko ya basu jari domin su tsaya da ƙafafunsu, a maimakon yi musu aure.
To sai dai ɗan majalisar ya kare matakin da cewa taimakon yaran ya yi, yana mai cewa galibinsu marayu ne waɗansa suka rasa iyayensu sakamakon matsalar tsaro da wasu sassan jihar ke fuskanta.
Wannan lamarin dai na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a Nijeriya da martani daga ɓangarori da dama, har ma daga baya wasu suke cewa ministar ta janye ƙarar da ta shigar bayan wasu sarakuna daga jihar ta Neja sun sa baki.
To sai dai a wata sanarwa da Ministar ta wallafa a shafinta na X ta bayyana cewa ba ta janye ƙarar ba.
Ta bayyana cewa, “bayan sa bakin Etsu Nupe Mai Martaba Alhaji Yahaya Abubakar da kuma ziyarar Sarkin Kontagora Mai Martaba Alhaji Mohammed Muazu da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, Abdulmalik Sarkindaji, a yanzu muna nemo hanyoyin da za mu warware wannan taƙaddama.
“Amma har yanzu umarnin kotu yana nan, ban janye ƙarata ba, har sai mun warware wuraren da suke da ƙura,” a cewar sanarwar.
Ta ƙara da cewa daga cikin shirin da take yi wa ‘yan matan marayu su 100 na Neja akwai ganawa da su da ɗaukar bayanansu, da mayar da su makaranta, da koya musu sana’o’i da shigar da su cikin shirin ma’aikatar na kasuwancin zamani ta hanyar intanet da kuma ba su tallafi.