Zauren Hadiza Gabon, wato Gabon’s Room Talk Show na ci gaba da shan suka da caccaka musamman daga wajen ’yan jarida da masu bibiyar lamura.
A shirin na Hadiza Gabon, tana gayyatar ’yan fim ne, sannan ta yi musu tambayoyi suna amsawa cikin nishadi.
- Maciji ya kashe kwamandan ’yan ta’adda a Borno
- JAMB ta kayyade mafi karancin makin samun gurbin karatu a bana
Sai dai wasu suna ganin jarumar ba ta bin dokokin aikin jarida, sannan suna cewa tana titsiye bakin da ta gayyata.
Lamarin ya fi tayar da hazo ne bayan tattaunawarta da mawaki El-Mu’az Birniwa, inda a cikin tattaunawar ta bayyana cewa kowa ya san cewa jaruma Hannatu Bashir budurwarsa ce kuma yana kai ta har gidansa, inda ta kara da cewa yaya iyalansa suke ji.
Sai ya amsa da cewa iyalansa sun san irin sana’arsa, don haka dole sun san zai yi mu’amala da mata.
Cikin kamar alamun fushi, sai mawakin ya ce ta ce kowa ya sani a lokacin, inda ta kara nanata cewa kowa ya sani, shi kuma ya ce tunda kowa ya sani mene ne amfanin yi masa maganar.
A karshe da ta yi masa tambayar sabanin da ya taba samu da tsohon Gwamna Nasir El-Rufa’i amma ya ki amsawa.
Ta nace sai ya amsa, sai ya fada cikin dariya cewa da ya san irin tambayoyin da za a yi masa ke nan, da bai zo ba.
A karshe tattaunawar, a wani abu kamar ramuwar gayya, shi ma mawakin sai ya tambaye ta cewa tana yawan kyauta da kudi, a ina take samun kudin.
Sai ta amsa da cewa tana sayar da kaya kuma tana sana’ar fim, sannan tana da wani kamfani da take harkokinta na gefe.
Sai ya kayar da baki ya ce ai ta dan ja baya a harkokin fim, sannan tana kyauta da kudin da wani furodusan zai iya shirya fim da shi.
Sannan ya san shagonta, har ma ya taba sayayya a ciki. Sai ta ce ai Allah ne Ya sa mata albarka a duk abubuwan da take yi.
Sannan ya ce to ai kamata a ce an san kamfanin nata ko watakila sai su kawo mutane a dauke su aiki, inda ta amsa da cewa idan sun gama tattaunawar za su yi magana.
Wadannan tambayoyi na Birniwa sun tayar da hazo, inda kamar an tabo inda yake yi wa wasu kaikayi ne, aka ta yada tsakuren bidiyon a kafafen sadarwa, musamman ganin cewa an sha yin zargin cewa ’yan wasan fim mata sun fi mazan kudi.
Aminiya ta ruwaito yadda tattaunawar jarumar da Rukayya Mousa ta tayar da kura, inda jarumar ta rika sharbar kuka a kan wani masoyinta, kuma mutane da dama suka yi zargin Hamisu Breaker ne, inda ta ce ta so, amma yanzu daukaka ta sa ya fi karfinta.
Ko a tattaunawarta da Rashida Mai Sa’a, bayan Hadiza Gabon ta yi mata tambayoyi, ita ma ta rama, inda ta ce me ya sa ake mata kallon tana da girman kai, kuma ko an kira ta fim ba ta ma daukar waya, ballantana ta shiga fim din?
Sannan a tattaunawarta da Maryam Malika, bayan ta gama amsa tambayar Hadiza Gabon kan ana zargin tana da rashin kunya, da ko kashe aurenta ta yi domin ta dawo fim?
Sai ita ma ta tambaye ta me ya sa suna tare a fim, ita ta yi aure, ta hayyafa, ta kuma dawo fim din ta same Gabon ba ta yi aure ba?
Sai ta amsa da cewa lokaci ne. Wannan ya sa masu bibiyar tattaunawar suke muhawarar shin wannan abin da jarumar take yi daidai ne a ka’idar aikin jarida?
Dokta Furera Bagel, marubuciya, kuma malama a Jami’ar Jihar Bauchi ta rubuta a shafinta na Facebook cewa, “Ina tunanin Hadiza Gabon ba ta san me ake nufi da Talkshow ba.
Watakila shirin Mehdi Hassan na HardTalk ko kuma wannan na tashar Channels din ne take kallo, inda ake tattaunawa da masu rike da madafun iko ake titsiye su.
Ko kuma tana kallon shirin Jerry Springers ne, inda mutane ke zuwa da kansu domin kwance wa kansu zane a kasuwa. Haba don Allah! Ai wannan cin mutunci ne da neman kashe aure!”
Shi ma dan jarida Aisar Fagge ya rubuta cewa, “Ya kamata jama’a su san wannan: Hadiza Gabon ba ’yar jarida ba ce, kawai tana magana a talabijin ne da mutanen da ta gayyata duk da cewa hirar da take yi da mutane na daya daga cikin aikin jarida.
“Amma jaridanci daban, surutu daban. A zamanin da muke ciki a Najeriya, magana a rediyo ko talabijin ba sai lallai mutum ya karanci wani ilimi na aikin jarida ba.
“Yawancin masu magana a rediyo da talabijin ba su da alaka ko kusa da karatun aikin jarida. Kawai masu magana ne don neman wani abu.”
Shi ma Sadik Tijjani Inuwa Bakori, malami a Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa, cewa ya yi, “Wai ku masu damunmu da zancen shirin Hadiza Gabon kun mance shirin ba kai-tsaye ake watsa shi ba ne?
“Idan ba tsabar son a fi mai kora shafawa ba ina ruwanku? Ta fi ku kusanci da mutanen da take gayyatowa tunda dai galibinsu ’yan wasan Hausa ne ko kuma masu alaka da Masana’antar Kannywood.
“ Hasali ma ba ta isa ta watsa shirin ba idan babu yardarsu. Bakinta ba su yi korafi ba, babu wanda ya ce an ci zarafinsa amma duk kun ishe mu da ce-ce-ku-ce da surutan kawai.
“Haba wannan wuce makadi da rawa har ina?” Sai dai malamin koyar da aikin jarida a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, Dokta Muhammad Hashim Suleiman ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa akwai irin aikin jarida da ake kira adversarial journalism, inda ya rubuta cewa, “Kafin ku fara ce-ceku-ce game da Hadiza Gabon, ya kamata ku san cewa akwai tsarin aikin jarida da ake kira Adversarial Journalism (titsiyewa), kuma shi ma aikin jarida ne.”
Malamin ya kara da cewa, “Idan ba ka shirya amsa tambayoyinta ba, kada ka amshi gayyatarta.”