✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zauna gari banza sun kashe ‘yan sanda 2 a Ondo

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ondo ta tabbatar mutuwar jami’anta biyu da fara hula daya sakamakon karbe zanga-zangar #EndSARS

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ondo ta tabbatar mutuwar jami’anta biyu da fara hula daya sakamakon karbe zanga-zangar #EndSARS da zauna-gari-banza suka yi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Bolaji Salami, ya bayyana  haka a lokacin da ya gabatar da wasu bata gari da ‘yan daba 18 ranar Talata a birnin Akure.

Ya ce, “’Yan sanda sun kama mutum 18 da ake zargi suna da aikata laifukan da aka yi a wurare daban-daban a fadin jihar nan.

“Daga cikin wadanda aka kama ana zarginsu ne da sata da kisa da taimakawa bursunoni suka tsare.

“Su kuma wadanda suka sace kayayyakin al’umma, suka kone gidaje, suka kashe mana abokan aiki, suka hana mu zaman lafiya, ina farin cikin shaida musu cewar doka ba ta barci kuma za ta yi aiki kan su,” inji shi.

Salami ya ce, an kashe ‘yan sanda biyu ne a Ore, karamar hukumar Odigbo da kuma garin Ondo, na karamar hukumar Ondo ta gabas.

Ya ce, an yi wa dan sanda daya kisan gilla ne a garin Ore, yayin da aka kashe abokin aikinsa a garin Ondo kafin aka kone shi cikin mota.

“Shi kuma farar hular da aka kashe na daga cikin mutum ukun da suka nemi yin fashi a wani banki cikin  birnin Ondo,” inji shi.

Salami ya ce, wadanda ake zargin sun yi amfani da zanga-zangar #EndSARS suka aikata laifukan sace-sace da kone-kone a sassa da dama na jihar.