Wata budurwa ’yar shekara 17 mai suna A’isha Ibrahim Isah da ke aji biyar a sakandaren Modibbo Adama a garin Maruda a Karamar Hukumar Kware a Jihar Sakkwato ta sha guba a yunkurinta na hallaka kanta saboda an laka mata satar Naira 1000.
Aminiya ta ziyarci Asibitin Murtala Muhammad a Unguwar Rogo inda aka kwantar da ita don jin ta bakinta kan dalilin da ya sanya ta sha guba. “Abin duniya ne ya ishe ni, yaya zan ji idan aka fada wa mahaifana wai na yi sata a makaranta ni da aka tura karatu? Na fada wa malamai ni ban dauki kudin kowa a dakin kwanan dalibai ba, amma suka ki aminta, wai za su kawo ni gaban taron dalibai a fada musu ni barauniya ce,” inji A’isha.
Ta ce ta yi kuka sosai tare da rantsuwa da Allah cewa ba ta taba sata ba kuma ba ita ta dauki kudin ba kuma ba ta ma san wanda ya dauka ba. “Duk abin da na fada musu ba su yarda ba, na shiga tashin hankali tun ranar Juma’ar da abin ya faru ban ci abinci ba har Litinin bayan na kaurace wa dakinmu da muke kwana kusan mu 20,” inji ta.
Ta ce “Da safe ranar Litinin ne na karbo fitilar hannu wajen abokiyata da nufin zan shiga bayan gida a ciki ne na cire batir guda na fitilar na huda shi na shanye, daga nan ban sake sanin halin da nake ciki ba sai kawai na gan ni a gadon asibiti. Ni ba zan koma makarantar ba, sai in iyayena ne suka tilasta ni in koma,” inji ta. “Idan shugabar makarantar ta sa maka karan-tsana to ba za ka sake jin dadin makarantar ba, haka aka taba yi wa Basira da Jamila sai da suka bar makarantar, ni gaskiya ba zan koma ba a kira min babana,” inji A’isha Ibrahim cikin kuka.
Ta ce ta yi nadamar shan gubar da ta yi don ta fahimci saura kadan ta sanya kanta cikin hallakar da tafi ta farko, sannan ta ce duk abin da aka yi mata ba za ta sake daukar mataki irin wannan ba. Ta ce fatarta ta samu lafiya a mayar da ita gida wurin mahaifanta.
Da wakilinmu ya tuntubi uwar dakinsu Amina Bawa Kebbe da ke kula da jinyarta a asibitin ta ce, “Kuruciya ce kawai ta dibe ta ta sha guba don an lika mata sata, ga shi an yi bincike an gano ba ta da wani laifi ba ita ta yi ba.”
Ta ce yarinyar ta tsora ta ne kan wata Malama Safiya ta ba ta tsoro cewa za a kawo ta gaban dalibai in ba ta fadi gaskiya ba, a Litinin da safe kawai ta sha gubar gudun kawo ta gaban dalibai kafin haka ta bar dakinsu kwana biyu.
Shugabar Makarantar Malama Shafa Musa ta ce yarinyar ba ta da lafiya ne, tana fama da zazzabin cizon sauro kuma su tara ne ta mayar da su gidajensu kan matsalar rashin lafiya.
Da wakilinmu ya bayyana mata binciken da ya gabatar kan lamarin kuma abin da ya gano ba shi ta fada ba, sai ta ce tana da magabata a wannan aikin wato Hukumar Kula da Ilimin Larabci da Addinin Musulunci su ke da alhakin yin magana ba ita ba.
Aminiya ta tuntubi Mataimakin Sakataren Hukumar Malam Ahmad S/Dogarai saboda sakataren hukumar yana hutu, inda ya ce shi bai da masaniya kan abin da ya faru a makarantar domin ba su samu wani rahoto kan yarinyar ba.
Duk kokarin jin ta bakin mahaifin yarinyar Malam Ibrahim Isa kan matakin da zai dauka kan abin da ya faru ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.