✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba ya yaba wa Tinubu kan sakin yaran da aka kama yayin zanga-zanga

Abba ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki nauyin karatun yaran domin inganta rayuwarsu.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu, kan sakin yara 76 da aka tsare bayan zanga-zangar yunwa.

Abba, ya gode wa shugaban ƙasa saboda tausayinsa da jin-ƙai wajen amsa kiran jama’a don tare da sakin yaran Kano.

Ya bayyana matakin a matsayin kyakkyawan shugabanci.

An yi taro kan sakin yaran a Fadar Shugaban Ƙasa, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya miƙa su ga Abba.

Da zarar sun dawo Kano, za a yi musu gwaji game da lafiyarsu sannan za a kula da su kafin miƙa su ga iyayensu.

Wannan wani ɓangare ne na shirin jihar don tallafa musu wajen farfaɗo da rayuwarsu da sake dawo da su cikin al’umma.

Abba, ya ce za a sanya yaran a makarantu, domin su samu damar sake gina rayuwarsu da bai wa al’umma gudummawa.

Ya jaddada cewa, duk da cewa laifukan da aka tuhumar su da su na da girma, amma a cewarsa akwai buƙatar sake ba su dama domin sake gina rayuwarsu.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Shettima ya bayyana cewa, an fara tsare yara 119 saboda rawar da suka taka wajen zanga-zangar da ta jawo asarar kuɗaɗe masu tarin yawa.

An saki 76 daga Kano, inda uku daga cikinsu tuni aka miƙa su ga iyayensu, yayin da aka miƙa wasu 39 ga Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna.

Abba, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kula da lafiyar yaran tare da ba su dukkanin goyon bayan da suke bukata don su samu nasarar sake gina sabuwar rayuwa.