Babban layin wutar lantarki na kasa a Nijeriya ya sake daukewa gaba daya a yayin da ake kokarin gyara layin da ya kawo wutar zuwa yankin Arewa.
Kamfanin Rararraba wutar lantarki na kasa (TCN) ya ce wutar ta dauke ne da misalin karfe 2 na ranar Talata.
Da misalin karfe 1 na rana karfin wutar da aka samar a layin shi ne megawat 2,711, amma zuwa karfe biyu karfin wutar ya tsiyaye gaba daya.
Kawo yanzu dai TCN bai bayar da bayan musabbanin daukewar wutar gaba daya ba.
- Zanga-zanga: Shettima ya gana da yaran da aka saki a Villa
- ’Yan Boko Haram na kwararowa Nijeriya daga Chadi
- Malaman addini na yaudarar mabiyansu saboda abin duniya — Sarkin Musulmi
Akalla karo na biyar ke nan da wutar lantarki take daukewa dungurungum a Nijeriya sakamakon lalacewar babban layin wutar na kasa.
Wanann na faruwa ne kasa da mako guda bayan dawo da wutar a jihohi 17 da ka yankin Arewa, bayan sun shafe sama da kwanaki 10 a cikin duhu saboda lalacewar babban layin wutar yankin daga Shiroro zuwa Kaduna.