✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zargin N6.3bn: Kotu ta wanke tsohon Gwamnan Filato, Jonah Jang

Kotun ta yi watsi da daukacin tuhume-tuhume 17 da aka gurfanar da tsohon gwamnan a kansu

Babbar Kotun Jihar Filato ta wanke tsohon gwamnan jihar, Jonah Jang, daga laifukan da ake gurfanar da shi a kansu, masu alaka da almundahanar Naira biliyan 6.3.

A ranar Juma’a ce, kotun ta yi watsi da daukacin tuhume-tuhume 17 da aka gurfanar da tsohon gwamnan a kansu a gabanta.

Kotun ta kuma wanke tsohon Babban Sakataren tsohon Ma’ajin Ofishin Sakataren Gwamna Jihar, Yusuf Pam, wanda aka gurafanar tare da tsohon Gwamna Jang kan zargin badakalar ta Naira biliyan 6.3.

Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) ce ta garfanar da su a kan zargin aikata laifuka 17 a lokacin da Jang yake Gwamnan Jihar Filato.

Zarge-zargen da aka gurafanar da su a kai sun hada da karkatar da Naira biliyan biy da Babban Bankin Najeriya (CBN) domin samar da sana’o’i da matasa da mata da masu kanana da matsakaitan sana’o’i.

Ana kuma zargin su da karkatar da wasu kudade da aka tanada domin samar da ilimi a matakin farko a jihar.

Amma da take yanke hukunci, alkalin Babbar Kotun Jihar Filato, Mai Shari’a Christy Dabup, ta ce EFCC ta kasa gabatar da kwararan hujjoji da za su tabbatar da laifin wadanda ake zargi.

Don haka ta ce babu wani laifi da mutanen biyu suka aikata na karkatar da kudade ko facaka da dukiyar gwamnati a lokacin mulkin tsohon gwamnan.

Daga nan sai ta yi watsi da zargin tare da wanke wadanda ake zargin saboda rashin hujjoji daga bangaren masu gabatar da kara.

Da yake magana bayan zaman kotun, lauya mai kare tsohon gwamnan, Mike Ozekhome (SAN), ya ce an yi adalci a hukuncin.