✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zargin kisa: ’Yan Sanda sun sa ladar N1m kan dan Majalisar Tarayya daga Bauchi

’Yan sanda sun yi alkawarin kyautar Naira miliyan daya ga duk wanda ya kawo dan majaisar, wanda ya shiga buya.

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya na neman dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bauchi, Yakubu Shehu,  ruwa a jallo, kan zargin kisa da tayar da zaune tsaye.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya kuma sanar da alkawarin kyautar Naira miliyan daya ga duk wanda ya kawo dan majalisar, wanda ya shiga buya.

Sanarwar ta ce ana neman dan majalisar ne “kan zargin kisa, hada baki wajen aikata laifi da kuma tayar da fitina da haddasa rauni da kuma tunzura jama’a.

“’Yan sanda na rokon duk wanda ke bayanin da zai taimaka a kama wanda ake zargin da kuma gurfanar da shi a gaban kotu, ya sanar da ofisin ’yan sanda mafi kusa ko ya kira lambar 08151849417 .

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa da farko dan Majalisar, wanda yanzu aka rasa inda ya boye, yana jam’iyyar PRP ne kafin daga bisani ya sauya sheka zuwa APC.

Hakan kuwa na zuwa ne kwanaki kadan bayan kotu ta bayar da belin dan Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, wanda aka tsare a gidan yari kan zargin kisa da tayar da fitina a lokacin zaben ranar shugaban kasa da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa daga aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.