✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zargin karkatar da tiriliyan 89.1 a CBN: Fadar Shugaban Kasa ta karyata Gudaji Kazaure

Fadar ta ce kwamitin da Gudaji yake ikirarin shugabanta ma haramtacce ne

Fadar Shugaban Kasa ta ce sam babu kamshin gaskiya a zarge-zargen da dan majalisa Gudaji Kazaure ya yi wa Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, na karkatar da kudaden da yawansu ya kai Naira tirliyan 89.1.

Gudaji Kazaure, dan Majalisar Wakilai daga jihar Jigawa a cikin wani bidiyo da ya karade intanet ranar Asabar, ya zargi Gwamnan na CBN da kokarin yin rufa-rufa kan badakalar kudaden na harajin shigo da kayayyaki daga kasashen waje.

Dan majalisar ya kuma yi zargin cewa da gangan wasu makusanta Shugaban Kasa suka hana shi ganawa da shi domin kada ya gabatar masa da sakamakon binciken nasa.

Kazalika, Gudaji Kazaure ya yi ikirarin cewa Buharin ne ya nada shi Shugabancin kwamitin a sirrance, domin ya gano badakalar da ke cikin binciken.

To sai dai a cewar Kakakin Buhari, Malam Garba Shehu, sam kwamitin da Gudajin yake ikirari haramtacce ne, kuma tuni Buharin ma ya rushe shi.

Sanarwar ta ce, “Da farko ma dai, kwamitin da dan majalisar yake ikirarin shugabanta ma haramtacce ne, an rushe shi tun tuni bisa umarnin Shugaban Kasar.

“Duk wanda ya san yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya yake zai yi mamakin yadda dan majalisa zai zama Sakataren kwamitin da yake karkashin bangaren Zartarwa.

“Baya ga haka, jimlar kudaden da ake hada-hadarsu a Najeriya baki daya da dukkan kadarorin da bankuna suka mallaka ba su kai tiriliyan 50 ba, ballantana ma a yi magana a kan wadannan kudaden da yake magana a kansu.

“Akwai kwamitin da Shugaban Kasa ya nada a watan Yunin 2020 wanda ke karkashin Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a da kuma Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Kasa (FIRS) da yanzu haka ke aikin tattara wadannan alkaluman kudaden harajin.”

Garba Shehu ya ce har yanzu kwamitin bai kammala aikinsa ba, kuma babu wata hujja da za ta gasgata zarge-zargen da ake yi wa gwamnati mai ci a kan hakan.

Ya kuma ce binciken da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa suka gudanar a kan lamarin ya nuna babu wata babbar matsala sabanin yadda ake zargin.

“Dangane da batun Gudaji Kazaure kuwa, ina mai tabbatar muku da cewa babu wani mahaluki da zai hana shi ganin Shugaban Kasa, saboda abokinsa ne.

“Yakan je ya gan shi a lokuta da dama, kuma ko yanzu muna maraba da shi ya zo ya gan shi,” inji Malam Garba Shehu. (NAN)