✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin garkuwa da mutane: Dan jarida zai bayar da shaida a kotu da bidiyon da ya nada

Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa a Karamar Hukumar Sabon Gari, ta gayyaci dan jarida domin ya bayar da shaida kan zargin…

Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa a Karamar Hukumar Sabon Gari, ta gayyaci dan jarida domin ya bayar da shaida kan zargin da ake yi wa wasu masu garkuwa da mutane.

Kotun ta kuma dage sauraron karar don bai wa lauya mai gabatar da kara damar gabatar da shaidar bidiyo da kuma dan jaridar da ya nadi hoton.

A shekarar ta 2021 ce dai dan jaridar, kuma wakilin Aminiya a Zariya, Aliyu Babankarfi ya nadi bidiyon inda ya tattauna da wadanda ake zargin.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Abdulkadir Sabo Mahmud ne ya dage sauraron karar zuwa 17 ga watan Yuli bayan da lauya mai gabatar da kara, Barista Dari Bayero ya shaida wa kotun cewa daya daga cikin shaidun da aka gabatar a zaman kotun ya ce akwai faifan bidiyo game da wanda ake zargin.

Ya kara da cewa a cikin wannan faifan bidiyon, wanda ake zargin ya fadi da bakinsa cewa ya aikata laifin a ofishin ’yan sanda.

“Kotu ta ba da umurnin a kawo faifan bidiyon da dan jaridar da ya dauka, wanda yanzu haka muna da shi,” a cewarsa.

A don haka sai lauya mai gabatar da kara ya ce yana da burin gabatar da karin wasu bayanai wanda hakan ya sa ya bukaci kotu da ta dage sauraron karar domin sanar da  lauyan wanda ake tuhuma a rubuce da kuma bai wa wakilin jaridar Aminiya da ya dauki faifen bidiyon damar halartar kotun domin ya ba da shaida.

Da yake yin tsokaci, lauyan wanda ake tuhuma, Nura Tukur, ya amince da dage sauraron karar.

Ana tuhumar Idris mustapha, da aka fi sani da Idi Maizomo da Isa ibrahim ne bisa zargin aikata laifuka 2 da suka hada da garkuwa da mutane.

Ana zargin su ne da laifin yin garkuwa da Ibrahim Yakubu da Yusha’u Sani da Abdullahi Mohammed Awwal (mai shekara 5) da Aisha Mohammed Awwal (mai shekaru biyu da rabi) dukkansu mazauna anguwar Nagoyi da ke Zariya a ranar 28 ga watan Janairun 2021.

Haka kuma, ana zargin wadanda ake kara da amsar kudin fansa har naira miliyan 14 kafin su sako wadanda suka yi garkuwa da su din.

Laifin da ake zarginsu dai ya saba wa sashi na 247(1) da na 246(c)na kundin dokokin Penal Code na jihar Kaduna na shekarar 2017.