✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zargin cin kudin makamai: An saki tsohon kakakin PDP daga gidan yari

Alkalin kotun daukaka kara a Abuja ya ce hukuncin da aka masa a baya ya saba da tsarin shari'a.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta saki tsohon kakakin jam’iyyar PDP, Olisa Metuh daga gidan gyaran hali na Kuje.

An saki Metuh ne a ranar Alhamis bayan umarnin da alkalin kotun, Mai Shari’a Nkeonye Maha ya bayar na ba shi beli har zuwa lokacin da za a ci gaba da shari’ar a ranar Laraba.

Lauyoyin Metuh, karkashin jagorancin Onyechi Ikpeazu (SAN) ne dai tun da farko suka gabatar da bukatar kotun ta sake shi, bayan Kotun Daukaka Kara a Abuja ta soke hukuncin da aka yanke masa a baya.

Lauyoyin nasa sun gabatar wa da kotun takardun hukunci da aka yanke masa a baya, ana washegarin ranar Kirsimeti.

Wani kwamitin alkalai uku wanda Mai Shari’a Stephen Adah ya jagoranta ya bayyana a ranar Talata, 15 ga watan Disamba cewa, hukuncin baya da Mai Shari’a Okon Abang ya yanke wa Metuh ba a yi shi bisa ka’ida ba.

A ranar 25 ga Fabrairun 2020 ne dai Mai Shari’a Abang ya yanke wa Olisa Metuh hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan kaso.

Kazalika, ya ci tarar Metuh Naira miliyan 375 tare da karbe kamfanin sa mai suna Destra Investment Ltd.

Sai dai Kotun Daukaka Karar ta amince da bukatun lauyoyinsa, inda ta ba da umarnin sakin sa.

Ana zargin Metuh ne da karbar kudi Naira miliyan 400 daga tsohon Mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Kanar Sambo Dasuki.

Metuh ya ce sun yi amfani da kudin ne wajen yakin neman zaben tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan.

%d bloggers like this: