Babbar Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba 1 da ke Jihar Bauchi ta sake tura Limamin Masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Jihar, Dokta Idris Abdul’aziz, gidan gyaran hali.
An dai sake tisa keyar malamin addinin Musuluncin busa nuna ‘raini ga kotu’, har zuwa nan da wata daya.
- Tinubu ya rushe dukkan hukumomin gudanarwar ma’aikatu da hukumomin gwamnati
- Tinubu ya kori dukkan manyan hafsoshin tsaro
Alkalin kotun, Malam Hussaini Turaki, ne ya bayar da umarnin ranar Litinin, kuma za a dawo da shi gaban kotun a ranar 19 ga watan Yuli.
Bisa wannan umarni, idan har ba wani umarnin na daban, malamin zai ci gaba da zama a gidan har zuwa ranar.
Tun da farko dai, Ma’aikatar Shari’a ta jihar Bauchi ce ta kai qarar Malamin, kuma aka kai masa sammaci, amma a ranar da za a shiga kotun ranar Laraba, 31 ga watan Mayun 2023 malamin bai samu halarta ba, inda lauyoyinsa sukace bayi da lafiya, suka kuma sanya takardar cewa kotin ba ta da hurumin sauraron karar.
Alkalin kotun ya kuma umarci jami’an tsaro da su kamo malamin a duk inda suka gan shi sakamakon kin bayyana a gaban kotu.
Ya kuma dage Shari’ar zuwa ranar biyar ga watan Yuni, inda a ranar lauyoyinsa suka bayyana suka ce wanda suke karewa ba shi da lafiya, shi ya sa bai bayyana ba.
Bayan da lauyoyin nasa suka gabatar da rahoton, sun roki kotun da ta janye tare da jingine umarnin da ta bayar na farko na cewa a kamo malamin duk inda aka gan shi.
Sai dai Alkalin ya dage zaman zuwa ranar ta Litinin, 19 ga watan Yuni, don yanke hukunci kan bukatar.
Tun da farko dai an kai Dokta Idris karar ce bisa zarginsa da munana ladabi ga Annabi Muhammad (S.A.W) tare da kokarin tayar da zaune tsaye.