✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin Atiku: Keyamo ya maka EFCC da ICPC a kotu

Keyamo ya dage kan lallai sai an gurfanar da Atiku a gaban kotu.

Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Festus Keyamo, ya maka hukumomin yaki da rashawa na EFCC da ICPC a kotu, yana mai neman a kama tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.

Babban lauyan, ya aike wa da EFCC da ICPC takarda kan lallai su kama dan takarar Shugaban Kasar na jam’iyyar PDP.

Ya ce ya kamata a kama Atiku a gurfanar da shi a gaban kuliya bisa laifukan da ake zarginsa na yin sama da fadi da dukiyar al’umma.

Keyamo ya gabatar da wannan bukata ce bayan wani faifan sautin murya da Michael Achimugu, tsohon na hannun daman Atikun ya fitar.

A cikin faifan da aka saki makonnin da suka gabata, Achimugu ya yi zarge-zarge da dama a kan tsohon Mataimakin Shugaban Kasar.

Ya yi ikirarin cewa daga shekarar 1999 zuwa 2007 a lokacin da Atiku yake Mataimakin Shugaban Kasa, ya hada baki da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo wajen halasta kudade.

A bisa wannan dalili ne Keyamo ya bukaci wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tilasta wa hukumomin yaki da rashawar su soma bincike tare da gurfanar da Atiku a gaban kuliya.