✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin almundahana: Sani Lulu ya kayar da EFCC a Kotun daukaka kara

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta yanke a ranar 22 ga Fabrairun shekarar…

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta yanke a ranar 22 ga Fabrairun shekarar 2016 a karkashin Mai shari’a E. S. Chukwu wanda ya yi watsi da bukatar da tsohon Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) hich dismissed a ‘no-case-submission’ filed by Sani Abdullahi Lulu, ya  gabatar a gabanta, cewa ta yi watsi da karar da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (FECC) ta kai a kansa da wadansu mutum uku tana zarginsu da almundahana.

A hukunci da ya yanke Alkalin Kotun Mai shari’a Ahmad Belgore ya ce: “daukaka karar ta cancanta, kuma an yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun ta yanke a ranar 22 ga Fabrairun shekarar 2016, kuma an wanke mai kara Sani Abdullahi Lulu tare da sallamarsa.”

Mai shari’a Belgore ya ce shari’ar daukaka kara ce a kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya ta yankin Maitama da Mai shari’a E.S. Chukwu ya yanke a ranar 22 ga Fabrairun shekarar 2016, inda aka yi watsi da bukatar mai daukaka kara ta a yi fatali da tuhumar da ake yi masa, bisa hujjar cewa wadanda ake kara sun bi ka’idar dokar bayar da kwangila don haka a ba su dama su kare kansu daga zargin da Hukumar EFCC take yi musu.

Lulu da mutum uku da suka hada da  Amanze Uchegbulam, tsohon Mataimakin Shugaban Hukumar NFF da Cif Taiwo Ogunjobi, wani tsohon dan kwamitin zartarwa kuma Babban Sakataren Hukumar NFF da Dokta Bolaji Ojo-Oba an gabatar da su ne a gaban kotu ranar 6 ga Satumban, 2010 bisa zargin almubazzaranci da kashe kudin hukumar ba tare da bin ka’ida ba a lokacin gasar kwallon kafa ta cin Kofin Duniya da aka yi a Afirka.

Lulu da abokan zarginsa an kuma zarge su da karya ka’ida wajen sayen motocin bas kirar Marcopolo ga kungiyoyin kwallon kafa na kasa. 

Yayin da daukaka karar Amanze Uchegbulam da Cif Taiwo Ogunjobi, da ake zarginsu tare da Sani Lulu ke gaban Kotun daukaka karar, wanda ake zargi na hudu, Bolaji Ojo-Oba, an riga an wanke shi tare da sallamarsa daga shari’ar.