Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta bayar da belin tsohon Akanta-Janar, Ahmed Idris kan zargin yin sama da fadi da Naira biliyan 109.5.
Kotun ta kuma dage sauraren shari’ar har zuwa ranar 10 da 11 ga watan Agustan 2022.
- Rikicin Ukraine: Shugabanni Afirka Munafikai ne –Macron
- Sarkin Daura mai ya sake auro budurwa mai shekara 22
Sauran wadanda ake tuhumar sun hada da Olusegun Akindele, Mohammed Usman daga kasuwar Gezawa.
Tun farko dai hukumar EFCC ce ta gurfanar da su a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume 14 da ake zarginsu da su wajen karkatar da Naira biliyan 109.5.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Adeyemi Ajayi, ya tsayar da ranar ne biyo bayan bukatar dage sauraren karar da lauyan wanda ake tuhuma, Chris Uche, (SAN) ya yi, domin tattaunawa da wadanda ya ke karewa.
Tun da farko alkali ya bayar da belin wadanda ake tuhuma, sannan EFCC ta gabatar da wani shaida Hayatudeen Ahmed wanda ya binciki lamarin.
Shaidar ya ba da labarin yadda ake biyan kudi da wani wuri zuwa wani, kuma an gabatar da takardun bogi don tabbatar da fitar kudaden.
Sai dai lokacin da ake shari’ar, lauyan wanda ake kara, Uche, ya roki kotun da ta ba su kankanin lokaci domin tattaunawa da wanda yake karewa.
Uche ya kara da cewa takardun da masu gabatar da kara suka gabatar sun yi yawa don haka akwai bukatar tattaunawa da wadanda yake karewa.
EFCC ta zargi cewa tsakanin watan Fabrairu zuwa Disamba, 2021
Idris ya karbi kyautar Naira biliyan 15 daga hannun Olusegun Akindele, a matsayin kyautar kashi 13 cikin 100 na kudaden da aka samu daga jihohi tara da ake hako mai a na gwamnatin tarayya ta ofishin Akanta-Janar na tarayya.
Kazalika, ta yi zargin cewa an core N84,390,000,00 daga asusun gwamnatin tarayya daga Fabrairu zuwa Nuwamban, 2021.
EFCC ta ce laifin ya saba wa sashe na 155 da na 315 na kundin ‘Penal Code’ karkashin dokar 532 na Najeriya na 1990.
Wadanda ake tuhumar duk sun musanta laifin da ake tuhumarsu da shi.