✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zangar tsadar rayuwa ta barke a Ibadan

Daruruwan mutane a garin Ibadan sun mamaye tituna a garin Ibadan domin gudanar zanga-zangar lumana kan tsadar rayuwa a fadin Najeriya

Da sanyin safiyar yau Litinin ne daruruwan mutane maza da mata suka fito dauke da rubutattun kwalaye a birnin Ibadan hedikwatar Jihar Oyo suna zanga-zangar lumana domin nuna damuwa kan tsadar rayuwa da ta shafi kasa baki daya.

Wasu daga cikin rubutattun kwalayen na kira da ‘A kawo karshen tashin farashin kayan abinci’, ‘Muna bukatar mulkin soja a yanzu’, ‘A sama mana kayan abinci da kula da lafiyarmu da sauran bukatun yau da kullum’, ‘Mun yi kuskuren zaben shugaban kasa’.

Aminiya ta halarci unguwar Mokola Round-About a birnin na Ibadan inda masu zanga-zangar ke rera wakokin batunci ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

Ana gudanar da zanga-zangar ta Ibadan ce a gaban ’yan sanda da sauran hukumoin tsaro da suke dauke da bindigogi da sauran kayan aikin ko-ta-kwana.

Aminiya ta gano cewa sanarwar fara wannan zanga-zangar ta fito ne da yammacin Lahadi da aka watsa ta intanet ba tare da sunan mutane ko kungiyar da ta shirya gangamin ba.

Hakan ne ya sa rundunar ’yan sandan Jihar hanzarta girke jami’anta a unguwar ta Mokola Round-About da ke kusa da ofishin gwamna da sakatariyar gwamnati domin guje wa barkewar rikici.