Wasu matasa mambobin jam’iyyar PDP a ranar Litinin sun fantsama titunan Babban Birnin Tarayya Abuja suna zanga-zangar neman Uche Secondus ya sauka daga shugabancin jam’iyyar.
Matasan, karkashin wata inuwa da ta kira kanta mai fafutukar ceto jam’iyyar daga bisani dai ta tafi har zuwa shalkwatar PDP ta kasa don nuna rashin jin dadinta kan yadda a ’yan kwanakin nan wasu gwamnoninta suka sauya sheka zuwa APC.
Sun dai rika daga kwalaye dauke da rubuce-rubucen nuna Allah-wadai da kuma yanke kauna ga shugabancin na Secondus, tare da shawartarsa da ya yar da kwallon mangwaro ya huta da kuda.
Da yake jawabi ga ’yan jarida a sakatariyar jam’iyyar, jagoran masu zanga-zangar, Kwamared Tamunotonye Inioribo ya ce ajiye mukamin shugaban a kashin kansa shi ne zai share fagen sake fasalin PDP kafin zabukan 2023 masu zuwa.
Sun dai zarge shi da raba kan ’ya’yan jami’yyar don biyan bukatar kashin kansa, inda suka ce sakacinsa ne ya jawo har Gwamnonin jam’iyyar masu ci guda uku da Sanatoci da dama suka sauya sheka.
Sakamakon irin halin da jam’iyyar ta tsinci kanta a ’yan kwanakin nan dai, shugabancinta sai da ya kira taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da nufin magance su.
Ko da yake an cimma matsaya kan kafa kwamitin sulhunta ’yan jam’iyyar, har yanzu ba a daddale batun neman Secondus din ya suka daga mukaminsa ba.
A wani labarin kuma, Gwamnonin jam’iyyar yanzu haka suna can suna wani taro a masaukin Gwamnan Jihar Akwa Ibom da ke unguwar Asokoro a Abuja don lalubo bakin zaren.
Taron dai na gudana ne karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, wanda kuma shi ne shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar.