✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zangar neman dawo da Aminu Bayero karagar mulki ta ɓarke a Kano

Ana ci gaba da shiga ruɗani a Kano kan rushe masarautu da gwamnatin jihar ta yi.

Magoya bayan Aminu Ado Bayero sun fara zanga-zanga a kan titin zuwa gidan gwamnatin Jihar Kano, inda suka buƙaci a mayar da tsohon sarkin kan karagar mulki.

Ana ci gaba da shiga ruɗani a Kano, yayin da jihar ke da sarakuna biyu, duk da rushe sarakunan da majalisar dokokin jihar ta yi a ranar Alhamis.

Da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Lahadi, matasa ɗauke da kwalaye suka mamaye tituna tare da buƙatar a dawo da Aminu Ado a matsayin Sarkin Kano.

Wasu daga cikinsu sun ƙone tayoyi a kan tituna yayin da wasu ke rera waƙoƙin adawa da gwamnati.

Aminiya ta hangi ‘yan sanda a kan titunan amma ba su yi yunkurin tarwatsa masu zanga-zangar da ke tattaki zuwa fadar da Sarkin Sanusi II yake ba.

Masu zanga-zangar sun gudanar da salloli tare da addu’ar alƙunutu kafin daga bisani suka hau kan tituna don nuna rashin jin daɗinsu game da matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka.

Wasu daga cikinsu na riƙe da kwalaye ɗauke da rubuce-rubuce kamar haka: “Abba Kabir Yusuf, ka bi umarnin kotu”, “Kotu ce ta ba ka mulki”, “Dole ne ka yi biyayya ga kotu”, “Har yanzu Aminu ne sarkinmu”, “Muna adawa da rashin adalci.”

Idan ba a manta da sanyin safiyar ranar Lahadi ne, wasu gungun matasa suka gudanar da zanga-zanga a masarautar Gaya don nuna fushinsu kan rushe masarautar da aka yi.