A yayin da ake can ana gwabza yakin a Ukraine biyo bayan hare-haren da Rasha ta kaddamar, a can kuma Rashar ana ta samun karuwar masu zanga-zangar kin jinin yaki a kusan garuruwa da birane 40 a fadin kasar.
Hotunan bidiyo da aka sanya a shafukan intanet na nuna daruruwan mutane na maci suna cewa ba sa son yaki a Moscow da St-Petersburg da Siberia da Yammacin Rasha.
- Ukraine ta nemi kasashen duniya su dauki mataki kan mamayar Rasha
- Jama’a na neman mafaka a Ukraine saboda firgici bayan mamayar Rasha
A kalla mutum 735 aka kama a wuraren wadannan zanga-zangar a fadin Rasha a ranar Alhamis, da suka hada da fiye da 330 a Moscow, a cewar OVD-Info, da ke bin diddigin wadanda aka kama a zanga-zangar ’yan adawar.
BBC ya ruwaito cewa an ga hotunan dandazon mutane a kusa da fadar Kremlin ta Rasha.
Rahotanni na cewa an samu barkewar mummunan fada a gabashin Ukraine bayan da dakarun Rasha suka kutsa kasar.
Ukraine ta ce manyan motocin yaki na Rasha sun shiga kasar ta wurare da dama, ciki har da ta yankin Crimea da ta mamaye sannan kuma da Belarus daga bangaren Arewa.
Mazauna birnin na biyu mafi girma a kasar, Kharkiv, sun ce ana jin tagogin gidaje suna ta girgiza, sakamakon barin wuta da rokoki da ke ta fashewa, a ba-ta kashin da aka fara tsakanin sojojin Ukraine din da na Rasha.
An bayar da rahoton mutuwar farar hula ‘yan Ukraine sama da 30, wadanda suka hada da akalla mutum 18 da aka kashe a kusa da tashar jirgin ruwa ta Odessa a wani hari na makami mai linzami.
Gwamnatin Rasha ta ce ta kai hare-hare da makami mai linzami a kan sansanonin soji da filayen jiragen sama da suka hada da, babban filin jirgin sama na Kyiv da kuma filin jirgin Ivano-Frankivsk da ke yammacin kasar.
Da yake sanar da kaddamar da farmakin na soji Shugaba Putin ya yi gargadin cewa duk wani tsoma baki ko katsalandan da wata kasa za ta yi, za ta gamu da martanin da ba ta taba gani ba a tarihi.
A martaninsa Shugaban Amurka Joe Biden ya ce za a dora wa Rasha alhakin duk abin da ya biyo baya kan harin da ta kai ba gaira ba dalili.
A nan gaba ne zai yi jawabi kan matakin da Amurka za ta dauka a kan Rashar.
Dan majalisar dokoki na Demokrat Jim Himes wanda ke kwamitin bayanan sirri ya ce manufar ita ce mayar da Rasha saniyar ware a duniya.
Ya ce Amurka za ta yi ainahin abin da ta yi alkawari, kuma Shugaban kasa zai tabbatar da hakan yau, wanda shi ne abin da za mu yi jagora da shi, abin da muke fata zai kasance tsattsauran takunkumin tattalin arziki.