✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zanga-zangar kin jinin rigakafin COVID-19 ta kara zafi a Belgium

Zanga-zangar dai ta haifar da taho-mu-gama tsakanin mutane da ’yan sanda.

’Yan sanda a kasar Belgium a ranar Lahadi sun yi amfani da ruwan zafi wajen tarwatsa masu zanga-zangar kin jinin rigakafin COVID-19 da take karuwa a kasar.

Kasar dai da ma wasu kasashe da dama a nahiyar Turai na ci gaba da fuskantar tirjiya kan matakin da aka dauka na tilasta wa mutane yin allurar rigakafin.

Akalla mutum 8,000 ne suka yi tattaki a birnin Brussels, babban birnin kasar, zuwa hedkwatar Tarayyar Turai suna rera wakokin neman ’yanci.

Sai dai gidan talabijin na Aljazeera ya rawaito cewa adadin bai kai na mutum 35,000 da suka yi zanga-zanga kan rigakafi da kuma sake kakaba dokar kulle a watan da ya gabata ba.

An dai yi amfani da shinge tare da girke jami’an tsaro wajen hana masu zanga-zangar kaiwa ga shatale-talen hedkwatar ta Tarayyar Turai.

Wasu jirage biyu marasa matuka da kuma wani jirgin mai saukar angulu dai sun yi wa masu zanga-zangar rumfa, inda suka rika fesa ruwan zafi ta sama.

Lamarin ya kuma kara kazancewa ne bayan ’yan sanda sun fara jefa barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar, lamarin da ya haifar da taho-mu-gama tsakaninsu da ’yan sandan.