Hargitsin da zanga-zangar #EndSARS ta haifar a Jihar Oyo da ma wasu sassan kasar nan, ya janyo kulle dukkannin makarantu a fadin jihar.
Duk da dai gwamnatin jihar ba ta ba da umarnin rufe makarantun ba, amma shugabannin makarantun sun dauki matakin rufe su ne saboda halin fargaba da malamai da dalibai suka tsinci kansu a ranar Litinin.
- Tinubu ya ba masu zanga-zangar #EndSARS hakuri
- An sanya dokar hana fita a Legas
- ’Yan daba sun tarwatsa zanga-zangar #EndSARS a Kano
Makarantun da suke na gwamnati kuwa sun bude, amma ba a samu zuwan dalibai da dama ba.
Wasu daga cikin malamai kuwa ba su samu damar shiga makarantun ba sakamakon rufe manyan hanyoyi da masu zanga-zanga suka yi a jihar.
Wasu manyan titunan garin da masu zanga-zangar suka kulle sun hada da babban titin Ibadan, sai kuma titin Olodo da kuma titin Iwo.
A wani bangare na jihar an samu barkewar rikici tsakanin masu zanga-zangar da kuma masu sana’ar sufuri.
Masu sana’ar sufurin na zargin masu zanga-zangar da kawo musu koma baya wajen samun abin da za su rufa wa kansu asiri.