Daya daga cikin fitattun malaman Islama a Najeriya kuma Babban Limamin Masallacin Usman bin Affan da ke Kano, Dakta Abdullah Gadon Kaya, ya ce zanga-zangar #EndSARS na neman ta rikidewa zuwa rikicin addini.
Shehin malamin ya bayyana hakan ne cikin wani sakon sauti da ya wallafa ranar Lahadi a shafinsa na Facebook.
- Dan marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ya rasu
- Buhari ya fadi adadin mutanen da aka kashe a zanga-zangar EndSARS
Dokta Gadon Kaya, ya wallafa sakon da taken ‘Sakon Gaggawa na musamman a kan zanga-zanga a Nigeria’.
Ya ce zanga-zangar #EndSARS na neman rikidewa zuwa yaki da Musulunci da Musulmai ta hanyar kashe Musulmai haka kawai, inda aka yi musu kisan gilla da lalata dukiyarsu, musanman a yankin Kudu.
Malamin ya zargi masu zanga-zangar da cewa suna yi ne da wata boyayyar manufa ba ta neman gyara kasa ba.
“Da manufarsu ta gaske ce da lokacin da aka rasa zaman lafiya a jihohin Maiduguri da Zamfara da Katsina da an ji sun fito suna Allah-wadai da yanayin rashin tsaron amma ba su iya yin hakan ba.”
Ya kuma yi takaicin yadda Gwamnatin Tarayya ta fifita bukatar mutanen Kudu da amsa kokensu cikin gaggawa duk da cewa an karbi bukatar tasu ta soke rundunar SARS.
Dokta Abdullah, har ila yau ya yi kira da “Lallai Gwamnatin Tarayya ta tabbatar ta ba wa Musulman da ke yankin Kudancin kasar nan kariyar rayukansu da dukiyoyinsu.
“Kuma ta yi yunkurin dakatar da wannan fitina a matsayinta na mai karfin ikon samar da tsaro da wanzar da zaman lafiya a fadin kasar nan”.
Ya ci gaba da cewa, “Babu alakar zanga-zangar da kashe Musulmi da kona masallatai, don haka a taka musu burki idan ba haka ba, muma da karfinmu.”
Malamin ya kuma ja hankalin ’yan Arewa da su san kansu, kuma su tsare jihohinsu.