Da safiyar ranar Lahadi ne aka tashi da zanga-zanga a kan titunan masarautar Gaya, ɗaya daga cikin masarautu biyar da majalisar dokokin Jihar Kano ta rushe.
Majalisar dokokin jihar dai ta soke dokar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya yi amfani da ita wajen tsige Muhammadu Sanusi II a shekarar 2020.
Yayin da yake amincewa da dokar a ranar Alhamis, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sanar da rushe ƙarin masarautau guda huɗu da Ganduje ya ƙirƙiro.
Masarautun da aka rushe sun haɗa da Rano, Gaya, Ƙaraye da kuma Bichi.
Gwamnan ya kuma umarci dukkanin sarakunan masarautun da suka haɗa da Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, Sarkin Gaya, da su miƙa al’amuran masarautunsu ga mataimakin gwamnan Jihar, Kwamared Abdulsalam Gwarzo, wanda ke kula da ma’aikatar ƙananan hukumomi da al’amuran sarakuna.
Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa Sarkin da aka tsige ya fice daga fadar da tsakar daren ranar Alhamis.
Babu wata alamar tashin hankali ko tarzoma a garin bayan an girke jami’an tsaro dauke da makamai.
Wani mazaunin garin, Abubakar Shuaibu, ya ce wasu mutane ba su ji daɗin rushe masarautar ba.
Amma da safiyar ranar Lahadi, mazauna yankin sun tururuwa inda suka nuna rashin jin daɗinsu kan rushe masarautar.
Masu zanga-zangar sun yi zargin an musu rashin adalci, inda suka ce rushe masarautar na da nasaba da siyasa.