Zanga-zanga ta barke a rana ta biyu bayan kayen da Shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya sha a babban zaben kasar da aka yi wanda har yanzu bai amince da sakamakon ba.
’Yan sanda na ci gaba da harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar da suka toshe manyan tituna a Brasilia, babban birnin kasar.
- Zan soke biyan kudin NECO da JAMB, zan dauki sojoji 750,000 —Kwankwaso
- Farashin amfanin gona a kasuwannin Arewa
Sa’o’i 36 bayan sakamakon da ya nuna cewa ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Lahadi da maki 1.8 kacal, har yanzu Bolsonaro bai ce uffan ba.
Bayanai sun ce wannan lamari na kara nuna damuwarsa kan cewa yana iya kokarinsa ya kalubalanci sakamakon bayan shafe watanni yana kai hari kan tsarin zaben da aka ayyana a matsayin magudi.
Kamfanin Dillancin Labari na AFP ya ruwaito cewa, a yankin Novo Hamburgo da ke kusa da Kudancin birnin Porto Alegre, ’yan sanda sun harba barkonon tsohuwa don tarwatsa wata zanga-zangar.
Babban Daraktan Hukumar ’Yan Sandan babban birnin kasar, Marco Antonio Territo de Barros, ya shaida wa taron manema labarai a Brasilia cewa, an samu toshewar tituna 267 a fadin kasar.
Masu zanga-zangar sanye da tutar Brazil, sun nuna rashin jin dadinsu da sakamakon zaben.
Tashin hankali na zuwa ne bayan yakin neman zabe mai cike da cece-kuce da aka yi tsakanin Bolsonaro mai ra’ayin mazan jiya da kuma magajinsa Luiz Inacio Lula da Silva.