✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zanga ta barke a Kudancin Najeriya saboda karancin sabuwar Naira

Bankuna da dama sun akatar da harkokinsu har sai kuma abin da hali ya yi.

Zanga-zanga ta barke a kananan hukumomin Uvwie da Warri ta Kudu a Jihar Delta saboda karancin sabbin takardun kudade da aka sauyawa fasali.

Aminiya ta ruwaito cewa zanga-zangar ta barke a ranar Juma’a inda mazauna yankunan da ke Kudancin kasar suka soma kone-konen tayoyi da rufe hanyoyi domin yi wa mahukunta bore.

Wannan dai na zuwa ne sa’o’i bayan makamanciyar zanga-zangar ta barke a birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Lamarin dai ya sanya bankuna da dama sun rufe sun dakatar da harkokinsu har sai kuma abin da hali ya yi.

Bayanai sun ce masu zanga-zangar da suka hada har da mata ’yan kasuwa sun rufe hanyar Warri zuwa Sapele da kuma babbar hanyar Hukumar Kula da Tashohin Jiragen Ruwa ta Kasa.

Wasu masu zanga-zangar sun yi zaman dabaro domin hana ruwa gudu a Bankunan UBA da Union da ke daura da Babbar Kasuwar Warri.

Galibi dai masu zanga-zangar sun daga alluna masu dauke da sakon babatu da bayyana takaici dangane da yadda karancin sabbin takardun Naira ya kawo tsaiko a harkokinsu na kasuwanci.

Jami’an tsaro sun yi ta kai-komon kwantar da tarzomar da masu zanga-zangar ke kokarin tayarwa, amma lamarin ya gagari Kundila.

Wata mata mai tireda ta yi korafin yadda ta tashi babu ko asi a ranar Alhamis dalilin rashin ciniki a kasuwa.

“Yunwa ta addabi ’ya’yanmu saboda kasuwanci ya tsaya.

“Ba ma iya cirar kudi a banki, kuma ko turawa muka yi ta tiransfa ma ba ta tafiya.

“Idan mun bude shago ma ba a samun ciniki saboda hada-hadar kudin ta kowacce hanya ta tsaya.”