✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-Zanga: Rundunar sibil difens ta yi atisaye a Gombe

An gudanar da atisaye da nufin tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro.

Kwamandan rundunar tsaro ta sibil difens a Jihar Gombe, Muhammad Bello Mu’azu ya jagoranci jami’ansa atisayen zama cikin shirin ko ta kwana a jihar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, jami’an tsaron sun gudanar da atisayen nuna karsashi domin tabbatar da an samar da cikakken tsaro ga rayuka da dukiyoyin al’umma a dalilin zanga-zangar da aka shirya a ranar 1 ga watan Agusta.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Buhari Sa’adu ya fitar ta ce an gudanar da atisayen ne a bisa umarnin babban kwamandan rundunar na kasa Dokta Abubakar Ahmed Audi.

An gudanar da atisayen domin tanadar matakan tsaro a wurare masu muhimmanci don hana duk wani aikata laifi da karya doka da oda a kokarin tabbatar da kwanciyar hankali a yayin zanga-zangar.

“Wannan atisaye na nuni da ƙarfi da aka gudanar an yi shi ne domin tauna tsakuwa wanda aka fara daga hedkwatar rundunar zuwa unguwar Jekadafari da titin Abacha sannan aka ratso ta unguwar London mai Dorawa da sauran wurare.

“Hakan zai kara tabbatar da shirin rundunar da kuma jajircewarta wajen kare jama’a cikin kwarewa a kowane lokaci.”

Sanarwar ta ce Kwamandan ya shawarci matasa da su jingine zanga-zangar da suka shirya yi kuma su bi hanyoyin lumana wajen bayyana bukatunsu ga gwamnati.

SP Sa’adu ya jaddada cewa rundunar za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.