Majalisar Dattawa ta roƙi ’yan Nijeriya da su jingine zanga-zanga su bai wa Gwamnatin Tarayya ƙarin lokaci domin sauye-sauyen da take gabatarwa su haifar da ɗa mai ido tare da biyan buƙatunsu.
Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa gwamnatin ta fara biyan buƙatun masu zanga-zangar.
- ‘Gwamnoni da dama ba za su iya biyan N70,000 mafi ƙarancin albashi ba’
- An haramta zanga-zangar tsadar rayuwa a Ghana
Da yake nanata buƙatar ƙara wa gwamnatin lokacin domin manufofin da ta kawo su soma tasiri, Akpabio ya ce a tsawon shekara guda da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kan karagar mulki ya kawo sauye-sauye domin bunkasar tattalin arzikin ƙasar.
Ya ce daga cikin manufofin da gwamnatin ta kawo domin rage talauci ciki har da sanya hannu kan dokar sabon mafi ƙarancin albashi da ta rancen karatun ɗalibai da sayarwa matatu da ɗanyen mai da assasa hukumar bunkasa Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas da kuma bai wa ƙananan hukumomi ’yanci.
Ya ci gaba da cewa, a shirye majalisar take ta yi dokoki a kan batutuwan da za su kawo wa ’yan Nijeriya sauƙin rayuwa.
Roƙon na zuwa ne bayan da Majalisar Dattawan ta sake hallara bayan wata ganawar sirri da ta shafe kusan sa’o’i biyu a yau Laraba.