✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan yi maganin ’Yan Kalare —Gwamnan Gombe

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Gombe ya yi kira ga ’yan adawa da su zo a hada kai wajen gina jihar a samar mata ci…

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Gombe ya yi kira ga ’yan adawa da su zo a hada kai wajen gina jihar a samar mata ci gaba mai dorewa.

A jawabinsa bayan karbar ranstsuwar fara aiki a wa’adinsa na biyu, Gwmana Inuwa ya ce gwamnatin sa ba za ta raga wa ’yan Kalare da sauran masu laifi ba, don tabbatar da cewa al’ummar jihar sun yi barci idon su biyu a rufe.

“A bangaren tsaro, za mu dauki tsauraran matakai domin magance matsalar ’yan Kare da suka dawo, suna tada hankalin jama’a a duk ƙananan hukumomi.

“Za mu magance matsalar ta hanyar sabon shirin tsaro na “Operation Hattara” da muka bullo da shi da nufin dafa wa ƙoƙarin jami’an tsaro wajen tabbatar da tsaro a jihar.”

Inuwa ya bayyana cewa zai tabbatar da ya biya duk wani bashin giratuti na tsofaffin ma’aikatan da suka yi ritya a jihar kafin karshen wa’adinsa a shekarar 2027.

Ya zargi gwamnatin da ta gabace shi da rashin biyan garatuti ba tun daga shekarar 2012 har zuwa 2019 kama daga na kananan hukumomi zuwa na jiha amma shi a karon farko na shekararsa hudu ya biya bashin na shekara hudu kuma zai daura.

Ya Kara da cewa duk da ya biya na shekara hudu har yanzu akwai bashi amma zai yi kokarin ya biya kafin ya sauka.