Shahararren mai kudin nan na duniya kuma Shugaban Kamfanin Twitter, Elon Musk ya ce yana so ya sauya tambarin Twitter.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Elon Musk ya ce “Nan ba da jimawa ba za mu sauya wa Twitter tambari,”, ta hanyar musanya hoton tsuntsun da a yanzu ke mazaunin alamar shafin.
- Yadda ’yar shekara 3 ta zama miloniya daga zuwa sayen burodi
- Mutum 6 sun mutu bayan kwankwadar barasa
Ya bayyana cewa za a sauya hoton tsuntun da alamar harafin ‘X’.
Hamshakin dan kasuwar ya ce ya zabi sauya wa shafin tambarin ne domin tabbatar da shafin ya bambanta da kowanne.
Elon Musk ya kuma bayar da samfurin misalin yadda sabon tambarin shafin zai kasance, ta hanyar wallafa bidiyon sabon tambarin a shafinsa.
Mista Musk ya kuma kara da cewa idan ya sauya sabon tambari a cikin daren, washe gari zai sa ya fara aiki a fadin duniya.
Kamfanin Twitter ya sha caccaka a ’yan kwanakin nan bayan matakin da ya ce zai dauka na kayyade adadin sakonnin da mutum zai iya karantawa a duk rana.
Jim kadan bayan hakan sai kamfanin Meta da ke adawa da Twitter ya fitar da sabuwar manhaja mai suna Threads wadda miliyoyin mutane suka yi rajista.
Hakan ya harzuka shugaban kamfanin na Twitter inda ya sha alwashin shigar da kara a gaban kotu.
Tun can dama kamfanin na Twitter yana shan suka iri-iri kan wasu matakai da ya rinka dauka a baya.