Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce idan aka gudanar da zabe kuma ya fadi zai mika mulki ga wanda ya lashe zaben.
Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba, lokacin da yake tattaunawa ta musamman da wasu manyan ’yan jarida wadda aka watsa ta kai-tsaye ta gidan talabijin na kasa da gidan rediyon Najeriya.
Ya ce: “Idan har aka yi zabe sannan na fadi, tabbas za a rantsar da sabon Shugaban kasa. Najeriya ce mafi muhimmanci ba wani mutum ba. Kada a manta a shekarar 2011 na ce ni ne zan zama Shugaban kasar da zai mika mulki cikin ruwan sanyi idan na fadi zabe. Na yi alkawarin zan shirya zabe mai inganci a shekarar 2011, kuma da a ce na fadi a wannan shekarar zan mika mulki duk da cewa ban hau gadon mulki ba, a lokacin zan fi kwadayin in yi mulki don sunana ya shiga tarihi. Don haka idan na fadi zabe zan mika mulki.”
Shugaba Jonathan ya yi alkawarin za a yi zabe a Najeriya kuma za a rantsar da gwamnati a watan Mayu, 2015. “Ina tabbatar wa ’yan Najeriya za a yi zabe a kasar nan, za a kuma rantsar da sabuwar gwamnati a watan Mayu mai zuwa.”
Game da ko za a samu nasarar yakar Boko Haram cikin mako shida duk da cewa an shafe shekara shida ana fafatawa da su, Shugaba Jonathan ya ce daga bayan nan ya sayo sababbin makamai tare da samun goyon baya daga kasashen makwabta domin yaki da Boko Haram din. Ya ce kasar Chadi ta nemi amincewar Tarayyar Afirka kuma ta samu amincewa, yanzu tana tallafawa. Ya yi albishir din cewa nan da mako hudu ’yan Najeriya za su ga bambanci a wajen harkokin tsaro a Arewa.
Game da ’yan matan Chibok da aka sace kuwa, ya ce: “Ku ba mu karin lokaci… Kuma ina da yakinin labarin ’yan matan Chibok zai zamo mai dadi nan da ’yan makonni masu zuwa…. Za mu karbo su da ransu….”
Sai dai ya koka kan abin da ya kira sanya siyasa a cikin lamarin “Sai dai abin bakin ciki mutane suna sanya siyasa a cikin batun ’yan matan Chibok. Ba haka ake yi a sauran wurare ba. A sauran kasashe ana rusa katangar siyasa a lokacin da aka fuskanci harin ta’addanci, amma ba haka lamarin yake a Najeriya ba.”
Game da Dala miliyan tara da dubu 300 da aka kama a Afirka ta Kudu wajen sayo makamai Shugaba Jonathan ya ce kudin ba na Najeriya ba ne kai-tsaye. Kuma ya ce maganar tana gaban kotu.
Zan mika mulki idan na fadi a zabe- Jonathan
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce idan aka gudanar da zabe kuma ya fadi zai mika mulki ga wanda ya lashe zaben.Shugaba Jonathan ya…
