Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lashi takobin farfado da harkar wasanni a Najeriya ta hanyar gina filayen wasanni da yawa.
A cewar Atiku wannan salo ne ya kai kasar Maroko ga nasara tare da kafa tarihi a Gasar Kofin Duniya na 2022 da ke gudana a kasar Qatar.
- NAJERIYA A YAU: ’Yan Bindiga Sun Zafafa Hare-Hare Bayan Samuwar Mai A Bauchi
- Yadda ‘Cousin’ ke kawo tarnaki ga masoya
“Abin da muka gano shi ne Maroko ta gina filayen kwallo a kusan ko’ina a kasarta; Duk inda ka zagaya kauye, garuruwa da birane sun gina filin kwallo.
“Za ka ga yaro dan firamare da sassafe ya je ya buga kwallo kafin ya tafi makaranta, idan ya dawo da yamma ma zai sake bugawa,” kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya jaddada muhimmancin shigar daidaikun mutane harkar wasanni, ba wai kawai a bar wa gwamnati wuka da nama ba.
Ya ce zai bai wa masu son saka hannun jari a harkar wasanni dama don kawo sauyi da bunkasa tattalin arzikin da ke cikin harkar.
Idan ba a manta ba, Maroko dai ta kafa tarihin zama kasa ta farko a nahiyar Afirka da ta kai bantena matakin Wasan Kusa Da Karshe a Gasar Kofin Duniya, bayan doke Portugal da ci daya mai ban haushi.