Wani fitaccen dan siyasa a Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Umar Tsauri, ya sha alwashin zai katange dukkanin iyakokin kan tudu na jihar idan ya lashe zaben gwamnan jihar a zaben badi.
Alhaji Tsauri wanda kuma tsohon dan takara ne na jam’iyyar APGA a zaben gwamnan Jihar Katsina na shekarar 2015, ya ce zai katange jihar ce a wani yunkuri na tsare al’ummar jihar daga ir-iren kalubalen tsaro da take fama da shi a yanzu.
Wannan furuci dai na sa na zuwa ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da kuma taron kaddamar da majalisar yakin neman zabensa da aka gudanar a birnin Dikko kamar yadda Nigerian Tracker ta ruwaito.
Alhaji Tsauri ya sha alwashin kawo karshen matsalar tsaro musamman ta sace-sacen mutane da neman kudin fansa da ta addabi jihar tsawon shekaru, lamarin da ya ce katange jihar baki daya ita kadai ce mafita.
“Zan yi amfani da wasu dabaru na katange duk iyakokinmu da ke tsakanin Jihohin Zamfara, Kaduna da Kano.
“Sannan zan dauki ’yan sa-kai guda 500 a kowane yanki da matsalar tsaro ta tsananta,” inji Alhaji Tsauri.
A karshe, Alhaji Tsauri ya yi kira ga dukkanin jiga-jigan jam’iyyar da su kasance masu rikon gaskiya da amana a duk harkokin da suka sa gaba domin hakan a cewarsa ita kadai ce hanyar da za ta fidda jihar zuwa tudun mun tsira.