✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan daure shugabannin Kwadago shekara 21 –El-Rufai

El-Rufai ya ce zai yi wa shugabannin kwadago abin da ba za su kara marmarin Kaduna ba.

A yayin da zanga-zangar Kungiyar Kwadago ta kasa (NLC) take wuni na uku a Jihar Kaduna, Gwamna Nasir El-Rufai ya lashin takobin koya wa shugabannin Kwamared Ayuba Wabba da takwarorinsa darasi da ba za su kara kaunar shiga Kaduna.

El-Rufai ya ce shugabannin kwadagon manyan masu laifi ne kuma zai tabbatar da sun fuskanci hukuncin daurin akalla shekara 21 kan abin da suka aikata.

“Dukkannin wadannan masu taka doka, za mu koya musu darasin da ba za su sake marmarin shigowa jihar nan ba,” inji shi a jawabinsa ga  Taron Shekara-shekara kan Haraji karo na 23 wanda Cibiyar Kwararru kan Haraji ta Najeriya, CITN, ta shirya a Kaduna ranar Laraba.

Ya ce rufe bankuna da gidajen mai da makamantansu da ’yan kwadagon suka yi babban laifi ne da kuma karan tsaye ga doka, amma gwamnatinsa za ta wargaza yajin aikin ta kuma yi maganin ‘manyan masu laifin’.

Sannan ya nemi gafarar mahalarta taron kan yadda yajin aikin ya shafe su, da cewa ’yan kwadagon “Suna kokarin hana bude harkokin kasuwanci kamar bankuna da gidajen mai, wanda kuma babban laifi ne kuma za mu dauki mataki.

“Muna kokarin samar da tsaro ga dukkannin masu harkokin kasuwancin da ke son budewa.

“Ba ma adawa da ’yancin yajin aiki, kuna da damar yajin aiki, amma sai ku fice daga wuraren aikin domin aiki ya ci gaba da gudana koda ba tare da ku ba.

“Ba ku da damar rufe duk wata harkar kasuwanci; lallai ne mu dauki mataki mai tsauri kan mutanen da suka yi yunkurin yin hakan,’’ inji El-Rufai