Bayan kwanaki da bayyana cewa yana nan daram a kan takarar Gwamnan Jihar Kaduna duk da nuna dan takarar da Gwamna Nasir Ahmad El-Rufa’i ya yi, Alhaji Sani Mahmud Sha’aban, mai neman takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar APC ya kaddamar da ’yan kungiyar yakin neman zabensa na shiyyar Kudancin Kaduna, wanda aka gudanar a garin Kafanchan, hedkwatar Shiyya ta Uku.
Alhaji Sani Sha’aban ya nanata cewa tsayawa takararsa tana nan daram, kuma ya yi wa mutanen Kudancin Kaduna alkawarin ba su madafun ikon da aka saba kafin zuwan Gwamna El-Rufa’i, inda ya ce adalci shi ne bai wa kowane yanki kaso a mulkin dimokuradiyya ba tare da kallon addini ko kabila ko alkiblar siyasarsu ba.
- Dakarun MNJTF sun kashe shugabannin ISWAP 3 a gabar Tafkin Chadi
- El-Rufai ya haramta zanga-zanga a Kaduna saboda batancin da aka yi a Sakkwato
“Shi ya sa nake son fada muku gaskiya. Ya kamata ku dauki kanku a matsayin ’yan Jihar Kaduna da ke yankin Kudancinta ba tare da kallon addini ko kabilarku ba.
“Idan Allah Ya sa na samu mulkin Jihar Kaduna duk wanda na bai wa wani matsayi ko mukami na ga ba ya tabuka komai to kwana uku sun yi yawa zan sauya shi.
“Ina son ganin Jihar Kaduna ta zamo jiha mai cikakken tsaro da zaman lafiya. Kashe-kashe da sauran tashin hankali sun yi yawa kuma da yardar Allah za mu magance matsalar,” inji shi.
Ya ce lokaci ya wuce da wani zai zauna a daki ya zaba wa mutane wanda zai mulke su, inda yab ce hakan karya dimokuradiyya ce da karan-tsaye ga jam’iyya.
“Idan kuka bari aka yi amfani da ku wakilan jam’iyya kun zamo ba ku da amfani ke nan.
“Don haka, ina kira a gare ku da ku hada kanku ku yi abin da ya dace a lokacin zaben fid-da- gwani da ke tafe nan gaba kadan,”inji Sha’aban.
Shugaban ayarin yakin neman zabensa da aka rantsar a shiyya ta uku, Mista Yakubu Yatai daga Karamar Hukumar Kaura ya sha alwashin shiga lungu da sako don nema masa kuri’ar wakilan jam’iyya, inda kuma ya yi kira ga wakilan jam’iyyar su yi amfani da damar da suke da ita su zabi Sani Sha’aban don dawo da martabar dimokuradiyya tare da cin moriyarta, musamman a yankin Kudancin Kaduna.
Da yake bayani tun farko, Daraktan Yakin Neman Zaben Sani Sha’aban, Mista Ephraim Jatau, ya ce bai wa Sha’aban takara babbar nasara ce ga dimokuradiyya domin shi ne dan takarar da zai kai jama’ar jihar ga tudun-mun-tsira musamman a halin- ni-yasun da aka jefa jihar a ciki na rashin tsaro da yaudara da kabilanci da suka yi katutu a jihar.
Wani kusa a Jam’iyyar APC a Kudancin Kaduna, Farfesa Katuka Yaki ya ce yana goyon bayan dan takara Musulmi da zai dauki Kirista a matsayin Mataimakin Gwamna a Jihar Kaduna saboda dinke barakar da aka haifar a jihar da sunan addini.
Shugaban Jam’iyyar na Karamar Hukumar Jama’a, Alhaji Ibrahim Koli ya ce za su bai wa kowane dan takara dama duk wanda Allah Ya ba shi a zaben fid-da-gwani za su mara masa baya.
Wakilan jam’iyyar daga dukkan kananan hukumomin Kudancin jihar takwas ne suka halarci taron.