✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan daina tallafa wa Gombe United saboda rashin kataɓus — Inuwa Yahaya

Duk wata yana bai wa kungiyar ta Gombe United Naira miliyan 12.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya yi barazanar daina tallafa wa kungiyar kwallon kafar Gombe United saboda rashin katabus.

Gwamnan ya yi wannan barazanar ce a lokacin da yake korafi kan rashin kokarin Gombe United wacce a yanzu take na mataki 14 a teburin a gasar Firimiyar Najeriya (NPFL).

A cikin wata hirarsa da kafar talabijin ta jihar, ya ce duk wata yana bai wa kungiyar ta Gombe United Naira miliyan 12, amma babu wani sakamako mai kyau.

Gwamnan ya yi korafin cewa kungiyar Doma United da ma ba ta samun kudi daga gwamnati ta fi Gombe United kokari a fagen taka leda.

“Ko dai Gombe United ta zage damtse ta yi abin da ya dace ko kuma na yi watsi da su na koma Doma United domin dukan su kungiyoyin kwallon kafa ne a jihar.”