Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da nadin Alhaji Yakubu Muhammad Kwairanga a matsayin sabon Sarkin Funakaye.
Babban Daraktan Yada Labarai na Fadar Gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misilli, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Nadin sabon sarkin na zuwa bayan rasuwar Sarki Mu’azu Muhammad Kwairanga II, wanda ya riga mu gidan gaskiya a ranar 27 ga Agusta 2022.
Misilli ya bayyana cewa Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Ibrahim Dasuki Jalo, ya sanya hannu kan takardar nadin da aka bayar ga sabon sarkin, wanda zai maye gurbin marigayin.
A cewar kwamishinan, nadin ya yi daidai da damar da Kundin Tsarin Mulkin Jihar Gombe, ya bai wa gwamnan da tanadin Dokar Masarautun Jihar Gombe ta 2022 da kuma shawarwarin sarakunan masarautar Funakaye
Dasuki, a lokacin da yake mika takardar nadin ga sabon sarkin a fadar mai martaba da ke Bajoga a Karamar Hukumar Funakaye, ya bukaci sabon sarkin da ya dauki kowa a matsayin nasa tare da kulla alaka da duk wanda ke karkashinsa.
Yayin da yake godiya ga Allah Madaukakin Sarki, sabon sarkin ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar Funakaye da su mara masa baya.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da taka rawa wajen wanzar da zaman lafiya da hadin kan al’umma.
Da yake yi wa sabon Sarkin fatan zaman lafiya, kwamishinan, ya ce za a gudanar da bikin nadin sarautar tare da gabatar da ma’aikata ga sabon sarkin nan gaba kadan.